Turkiyya ta yi kunnen doki da Bosniya

Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya ta yi kunnen doki a wasan da ta buga a garin Rize da kungiyar kasar Bosniya.

FOTO_16611854_111020182254120000_R_SPO_20181011000000_aa-picture-20181011-16611854.jpg
Bidiyon wani bangare na wasan Turkiyya da Bosniya da aka tashi kunnen doki mara ci
Bidiyon wani bangare na wasan Turkiyya da Bosniya da aka tashi kunnen doki mara ci

Bidiyon wani bangare na wasan Turkiyya da Bosniya da aka tashi kunnen doki mara ci

Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya ta yi kunnen doki a wasan da ta buga a garin Rize da kungiyar kasar Bosniya.

Babu wanda ya samu damar jefa kwallo a raga amma a minti na 14 da fara wasa Bosniya ta kusa ta jefa kwallo daya tilo a ragar Turkiyya.

Dan waan baya Caglar Soyuncu ne ya yi kuskure inda kwallo ta kawace tare da tafiya hannun abokin hammayarsa Dzeko wanda ya mika wa Visca.

Viska ya samu kwallon tare da dukanta amma mai tsaron gida Sinan Bolat ya doke ta zuwa kwana.

A minti na 18 da fara wasan kuma danw asan Turkiyya Cengiz Under ya samu santsin wasa inda kwallo ta kubuce masa tare da fada wa hannun Zakaric amma mai tsaron gida Sinan Bolat ya doke ta da kafarsa zuwa kwana.

Bayan an dakko kwanar Visca ya bga ta zuwa waje.

A minti na 22 da fara wasan kuma Hakan Calhanoglu ya ja 'yan wasan bayan Bosniya inda ya buka shot daga nesa inda ta doke Sener Ozbayrakli tare da fita waje.

A minti na 28 kuma Cengiz under ya buda wani sho daga kusan mita 30 inda mai staron gidan Bosniya Sehic ya doke ta da hannu zuwa kwana.

A minti na 32 ma Turkiyya ta kusa jefa kwallo a raga. 

Hakan Calhanoglu ya bar wa Enes una kwallo ba tare da jiran Oguzhan Ozyakup ba.

Enes ya yi free daga shi sai mai tsaron gida amma ya buga kwallon zuwa waje.

A minti na 34 Oguzhan Ozyakup ya bayar da Pass mai kyau inda Calhanoglu ya kusa jefa kwallo.

Haka aka kammala wasan babu wanda ya yi nasara.Labarai masu alaka