Benzema ya samu rauni a cinyarsa ta dama

Dan wasan gaba na Faransa mai taka leda a kungiyar Real Madrid da ke buga wasanni a Gasar La Liga ta Spaniya Karim Benzema ya samu rauni a cinyarsa ta dama.

Benzema ya samu rauni a cinyarsa ta dama

Dan wasan gaba na Faransa mai taka leda a kungiyar Real Madrid da ke buga wasanni a Gasar La Liga ta Spaniya Karim Benzema ya samu rauni a cinyarsa ta dama.

Sanarwar da Kungiyar Real Madrid ta fitar ta ce, Benzema da dole ya fita daga wasa bayan bga rabin lokaci a wasanda suke yi da Alaves na gasar La Liga ya samu rauni a cinyarsa ta dama.

Kungiyar ta Real madrid ba ta bayyana yaushe dan wasan nata na gaba kuma na tsakiya zai warke ba amma ana sa ran zakaran na Faransa zai kauracewa filin wasa na makwanni 2.

Benzema da bai jefa wa Madrid kwallo ba a wasanni 4 da ta yi a baya-bayan nan ya kasance dan wasan da ya samu rauni bayan Marcelo, Isco da Carvajal.Labarai masu alaka