UEFA: Fenerbahçe ta lallasa Spartak Trnava da ci 2 da nema

A gasar UEFA ta Nahiyar Turai ƙungiya ƙwallon ƙafar Fenerbahçe wacce ke rukunin D ta lallasa abokiyar hamayyarta ta ƙasar Slovakia da ci biyu da nema.

Da farko da kochi Philip Cocu ya zaunar da Şener Ozbayrakli, Mehmet Topal da Benzia akan tebur. Haka kuma bai ɗauki ɗan wasa Aatif Chahechouhe ba.

A wasan da aka yi a filin Ulker Ƙungiyar ƙwallon Fenerbahçe ta fara da kwarin gwiwa.

An dai tafi hutun rabin lokaci ba tare da ko wacce kungiya ta saka kwallo a raga ba.

Bayan dawo wa hutun rabin lokaci Fenerbahçe ta yi nasarar jefa kwallo a raga.

A minti na 51 dan wasan Fenebahce mai suna Slimani ya jefa kwallo a raga.

A minti na 68 kuma wani dan wasan Fenebahce dan kasar Algeriya ya jefa kwallo na biyu a raga da kai.

Fenebahce ta yi nasarar a wasan da ci biyu da nema, inda ta kasance kungiya ta farko da ta fara yin nasara a rukunin D a gasar UEFA ta Nahiyar Turai a bana.Labarai masu alaka