'Yan majalisar dokokin Turkiyya sun lallasa na Kenya a wani kwallo da suka buga

'Yan majalisar dokokin Kenya sun yi rashin nasara a hannun takwarorinsu na Turkiyya da ci 3 da 1 a wasan kwallon kafa na sada zumunci da suka yi a Nairobi babban birnin Kenya.

Jakadan Turkiyya a Kenya Jamil Miroglu ya mika kambi ga 'yan majalisar na Turkiyya, kuma Kaftin din 'yan wasan Turkiyya dan majalisa mai wakiltar Istanbul Ali Sarikaya ya bayyana cewa, manufar wasan kwallon kafar ita ce a karfafa alakar da ke tsakanin kasashen 2.

Ya ce, irin wadannan abubuwa za su kara karfafafa alakar Turkiyya da Kenya da ta dauki tsawon shekaru 50.

Su ma 'yan majalisar Kenya sun nuna gamsuwa game da wasan inda suka tabbatar da cewa, takwarorinsu na Turkiyya na ba su gudunmowa sosai.

Dan majalisar Turkiyya Ali Sarikaya ne ya jefa kwallaye 2 a ragar Kenya sai Ibrhahim Yildiz da ya jefa kwallo 1 shi ma.

Daga bangaren Kenya kuma dan majalisa Malala Cleophas ne ya jefa kwallo a ragar Turkiyya.Labarai masu alaka