"Ku lullube ni da tutar Turkiyya,idan na yi shahada"

A duk lokacin da ya daura damar zuwa fagen gwagwarya a yammacin zirin Gaza, Muhammad Badwan na bar wa uwayensa wasiyya cewa, su lullube shi da tutar kasar Turkiyya,idan ya yi shahada.