"Donald Trump da Kim Jong-Un sun sasanta"

A 'yan kwanakin an dinka yada wani labari na sasantawar manyan makiya 2, shugaban kasar Koriya ta Arewa,Kim Jong un da takwaransa na Amurka,Donald Trump a kafafan yada labarai na duniya.

An yada bidiyon wasu mutane 2 masu kama da Trump da Kim, kamar an tsaga kara, wadanda suka dinka fitowa gaban manema labarai na duniya, da nufin yin da'awar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wadannan mutanen wanda a yanzu haka suke ci gaba farin jini a duniya, sun gayyaci Trump da Kim da su sansata da juna.

 


Tag: kim , trump