Trump ya gode wa shugaba Erdoğan

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gode wa takwaransa,Recep Tayyip Erdoğan,sakamakon sako fasto Andrew Brunson da kotun kasar Turkiyya ta yi.

Trump ya gode wa shugaba Erdoğan

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gode wa takwaransa, Recep Tayyip Erdoğan,sakamakon sako fasto Andrew Brunson da kotun kasar Turkiyya ta yi.

Trump ya wallafa wani sako na musamman a shafinsa na sada zumunta na Twitter.

Trump yaa sanar da cewa zai gana da fasto a zauren Oval Ofice da ke birnin Washington na kasar Amurka.

A sakonsa na Twitter Trump ya ce,"Sake ganin Fasto, babban farin cikin ne.Ina matukar godewa shugaba Erdoğan".

Haka zalika ya tabbatar da cewa, bai wa faston Andrew izinin fita waje zai sake karfafa alakar da ke tsakanin Turkiyya da Amurka.


Tag: trump

Labarai masu alaka