Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, Asusun bayar da lamuni na duniya IMF na sanya wa kasashe idanu tare da bin diddiginsu. Erdoğan ya sake jaddada cewa, bayar da ba shi ya dawo ta hanyar amfani da zinariya maimakon dalar Amurka. Ya ce, kasashen duniya manya ne suka kafa IMF kuma su suke juya kasashe tare da habaka hukumominsu. Ya ce, me ya sa a yayin taron G20 suke bayyana a bayar da ba shi da dala? ku zo a yi amfani da zinariya kawai. Dala na zama alakakai ga duniya. Ya kamata a kubutar da kasashen duniya daga sharrin dala. 

Babban labarin jaridar Star na cewa, mataimakin shugaban kwamitin tsarocna majalisar wakilai ta Rasha Aleksandr Sherin ya bayyana cewa,akwai bukatar su yi koyi da shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan wajen kare manufofin kasarsu. Sherin ya tattauna da kafar talabijin ta Rasha inda ya ce, idan ba su yi irin yadda Erdoğan ya yi ba to ba maka wa za su wahala kafin kubuta daga kaidin Amurka. Dole ne Rasha ta dauki misali daga shugaba Erdoğan na Turkiyya. Idan Rasha ta yi koyi da shi to za ta toshe bakin Amurka.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya mayar da martani ga kalaman shugagban kasar Faransa Emmanuel Macron na cewa, sun kai wa Assad hari tare da nesanta Turkiyya daga Rasha. Cavusoglu ya gudanar da taron manema labarai tare da Sakataren NATO Jens Stoltenberg da ya ziyarci Ankara inda ya ce, Macron ya so ya halarci taron Shugaba Erdoğan, Putin na Rasha da Ruhani na Iran suka shirya a Ankara amma aka kiamince wa da bukatarsa. Cavusoglu ya kuma ce, kasashe daban-daban sun karyata maganar da Macron ya yi, kuma Turkiyya na kira ga Macron da ya zama mai gaskiya.

Babban labarin jaridar haber Turk na cewa, Ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido ta Turkiyya ta bayyana shekarar 2018 a matsayin shekarar "Troy" wanda Hukumar Cigaban Ilimi da Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta amince da shi a matsayin kayan tarihi. Kamfanin Turkish Airlines ya nannade wasu jiragensa samfurin Airbus 321, TC-JTP da Airbus 321-200 da hotunan dokin na Troy.Labarai masu alaka