Islam addini ne na zaman lafiya

Firaministan Turkiyya,Binali Yıldırım ya kira kasashen Musulmai na duniya da su raya addinin Musulunci ta hanyar rungumar dabi'u nagari da ya zo mana da su.

Islam addini ne na zaman lafiya

Firaministan Turkiyya,Binali Yıldırım ya kira kasashen Musulmai na duniya da su raya addinin Musulunci ta hanyar rungumar dabi'u nagari da ya zo mana da su.

Yıldırım ya furta wannan kalamin a ranar Litinin da ta gabata a wani taro kan Musulmai marasa rinjaye na duniya,inda ya ce:

"Bai kamata mun manta da nauyin da ya rataya a wuyanmu wajen fidda hakkin mutanen duniya da kuma Musulmai tsirarru da ke cikinta.Kamata yayi mu adana zaman lafiyar da Islama ya za mana ta ita,tamkar jauhari.Lokaci ya zo da ya kamata mu hada kawunanmu, mu karfafa dangantakarmu,mu sake zage damtse don yakar yunwa da fatara a kasashen Musulmai".

Da ya tabo batun kyamar Musulunci a kasashen Yamma,firaministan ya ce:

"Jawabai na kyamar Musulunci da ake yadawa na ci gaba da yi wa zaman cude-ni-in-cude-ka, handinkai, da kuma cundanyarmu zagon kasa.Hakkokin bil adama da demokradiyya na ci gaba da zaizaya sabili bakar kyamar da ake ci gaba da nuna wa Musulmai.Idan ba a dauki matakan magance wannan matsalar ba, lamarin zai kai intaha".

Yıldırım ya ci gaba da cewa:

"Ba zamu taba yaki da kyamar Islama ba face sai mun yi watsi da rashin adalci,wariya da kuma yada farfaganda tsana da yin watsi da jama'a kan karyace-karyace".

Shugaban gwamnatin Turkiyya ya yi Allah wadai da yadda Turawa ke alakanta Musulunci da ta'addanci,inda ya ce:

"Mu Musulmai bamu kasakantar da wani addini don laifin da wani daga mabiyinsa ya aikata.Muna jiran a yi mana irin wannan kallon.Lokacin yin watsi da wariya da kuma cire bakin tambarin kyama da na ta'addanci da aka dangwala wa Musulmai,ya zo".

 Labarai masu alaka