Erdoğan: A nan gaba jama’ar Siriya ba su da kasar da wuce Turkiyya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, a nan gaba al’umar Kasar Siriya za su kasance ba su da wata kasa da ta wuce Turkiyya.

Shugaba Erdoğan ya yi jawabi a wajen taron jam’iyyarsa ta AKP a gundumar uskudar da ke Istanbul.

Ya ce, ya zuwa yanzu dakarun Turkiyya da suka fara kai hare-hare a Afrin da ke arewacin Siriya sun kassara ‘yan ta’addar aware na PKK/PYD-YPG dubu 4,163.

Ya ce, duk ‘yan ta’addar da za su yi wa Turkiyya barazana to haka za su yi musu, kuma ya zuwa yanzu sun kamo ‘yan ta’addar FETO 80 daga kasashen waje tare da dawo da su zuwa Turkiyya don fuskantar hukunci.

Erdoğan ya nuna muhimmancin da ke akwai wajen hada kan Mayakan Siriya Masu Zaman Kansu tare da sojojin Turkiyya inda ya ce, suna lalata wasan da ake yi a yankunansu, kuma a nan gaba Siriya za su kasance ba su da kasar da ta wuce Turkiyya. Dole ne a samar da yankunan zaman lafiya a Siriya ta yadda jama’ar Kasar za su koma Kasarsu.Labarai masu alaka