Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a ranar Talatar nan za a fara baje-kolin kasuwar kayayyakin harkokin sufurin jiragen sama ta Paris Air Show a filin tashi da saukar jiragen sama na Le Bourget. A baje-kolin za a nuna irin cigaban da aka samu a fannin sufurin jiragen sama. Turkiyya za ta nuna kayan da ta samar a kasuwar baje-kolin. A kasuwa jirgin bayar da horo da kamfani TAI ya samar zai jarraba tashi da sauka. A shekara mai zuwa ne ake sa ran jirgin zai fara aiki. Jirgin na da kujeru 12 nauyin tan 6 kuma sojoji da fararen hula za su iya amfani da shi. Turkiyya za kua ta nuna jirgi mai saukar ungulu samfurin T625 . Dadin dadawa kamfanin TAI zai sake nuna wa duniya jirgin yaki na T129 ATAK da kuma jirgi mara matuki na ANKA-S.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Kasashen duniya 11 da suka hada da Turkiyya sun shiga yarjejeniyar sayen jiragen yaki na F-35 guda 440. An bayyana cewa, yarjejeniyar ta tashi kan dalar Amurka biliyan 37 kuma abu ne da ya karya tarihi. Tun shekarar 2006 aka fara kirkirar jiragen yaki na fatalwa kuma za a nuna wa duniya su a kasuwar baje-koli da za a fara a birnin Paris a ranar Talatar nan. A makon da ya gabata kasashe 11 da ke son sayen jiragen suka gana a birnin Baltimore na jihar Maryland da ke Amurka inda suka kuma gana da hukumomin kamfanin Northrop Grumman da ya samar da jiragen na F-35. Kasashen sun hada da Turkiyya, Ostireliya, Isra'ila, Italiya, Holan, Koriya ta Kudu, Birtaniya da Amurka. 

Babban labarin jaridar Star na cewa, a karkashin yarjejeniyar da Turkiyya ta yi da Qatar suka yi. sojojin Turkiyya sun isa yankin Qatar. Sojojin na Mehmetçik za su yi atisaye tare da takwarorinsu na Qatar. Kafar yada labarai ta Aljazeera ta sanar da duniya cewa, dakarun Turkiyya sun isa Qatar kuma za su hada gwiwa da sojojin kasar don gudanar da babban atisaye.Kasashen da duniya sama da 10 da suka hada da Saudiyya, Bahrayn, Yaman, masar da Hadaddiyar Daular Larabawa sun yanke huldar jakadanci da Qatar sakamakon zarginta da taimaka wa ta'addanci. Bayan wannan rikici ne Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da kasar ta tura dakarunta zuwa Qatar.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, jirgin ruwa Aqua Stella ya tashi zuwa Gaza don kai kayan taimako ga falasdinawa dubu 10 da 600 da Isra'ila ta yi wa takunkumi tare da tsare su. Akwai kayan abinci, sha da magunguna a cikin jirgin ruwan. Haka zalika an dibi kayan wasan yara na yara guda dubu 18 da 100. Kayan karatu sinki dubu 32, kwalin abinci dubu 50, garin fulawa dubu 5, biskit da kek tan 100, kayan sa wa na mutu dubu 50, kayan Sallar idi dubu 1 da kekuna dubu 1 da goma.Labarai masu alaka