Saudiyya ta bayar da taimakon dala miliyan 100 ga 'yan ta'adda a arewacin Siriya

Masarautar Saudiyya ta sake bayar da miliyan 100 ga Amurka don amfanin 'yan ta'addar aware na YPG/PKK da ke arewacin Siriya wadanda suka mamayi yankunan da suke.

Saudiyya ta bayar da taimakon dala miliyan 100 ga 'yan ta'adda a arewacin Siriya

Masarautar Saudiyya ta sake bayar da miliyan 100 ga Amurka don amfanin 'yan ta'addar aware na YPG/PKK da ke arewacin Siriya wadanda suka mamayi yankunan da suke.

Jaridar New York Times ta rawaito cewa, ta bayar da labarin cewa, gwamnatin Saudiyya da ta shiga mawuyacin hali saboda batan dan jaridar Jamal Kashoggi ta bayar da kudin ga Amurka a lokacin da Ministan harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ke ziyara a Rasha.

Amurka ta dade tana neman wannan kudi amma yadda Saudiyya ta biya a lokacinda Pompeo ke yawon ziyara game da batan dan jaridar Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a ranar 2 ga Oktoba, na da jan hankali sosai.

Jaridar ta New York Times ta rawaito wani na cewa, wannan abu ba wai arashi ba ne kan yadda Amurka ke kallon manufofinta a Siriya.

Jaridar ta rawaito bayanin da mai ba wa Trump shawara kan yaki da Daesh Brett McGurk ya yi.

McGurk ya musanta cewa, biyan kudin na da alaka da ziyarar da Pompeo ke yi.

McGurk ya kare cewar tun watan Agusta Saudiyya ta yi alkawarin bayar da kudin kuma a watannin bzara aka sarna za a biya.

A watan Oktoban 2917 Ministan kasa na Saudiyya Samir Al-Sabhan ya ziyarci yankin Ayn ısa da ke rakka wanda 'yan ta'addar awaren na YPG/PKK suka mamaye.

Bayan wannan ziyara ne Saudiyya ta bayar da taimakon dala miliyan 100 don gyara gine-ginen da Amurka, YPG da PKKsuka rsa a lokacin da suka ce suna yaki da 'yan ta'addar Daesh.Labarai masu alaka