"Dala ce kawai kawar Amurka a fadin duniya"

Shugaban majalisar dokokin kasar Turkiyya Binali Yıldırım ya bayyana cewar kasar Amurka na ci gaba da rasa kawayenta a fadin duniya.

"Dala ce kawai kawar Amurka a fadin duniya"

Shugaban majalisar dokokin kasar Turkiyya Binali Yıldırım ya bayyana cewar kasar Amurka na ci gaba da rasa kawayenta a fadin duniya.

Binali Yıldırım, a yayinda yake jawabi a taron karawa juna sani da kungiyar haddin kan Musulmi ta shirya a birnin Geneva dake Switzerland:

A halin yanzu Amurka na ci gaba da rasa kawayenta a fadin duniya, a halin yanzu bata da wata babbar kawar da ta rage mata sai dalar ta.

Haka kuma ya sake korafi akan yadda Amurka ta hada kai da kungiyar ta'addar PYD/YPG a Siriya da sunan yakar wata kungiyar ta'addancin abinda ya kira abin ki da kyama.

 Labarai masu alaka