Zaftarewar kasa ta kashe mutane 12 a Kolombiya

Mutane 12 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa ta janyo a ‘yan kwanakin nan a Kasar Kolombiya.

Zaftarewar kasa ta kashe mutane 12 a Kolombiya

Mutane 12 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa ta janyo a ‘yan kwanakin nan a Kasar Kolombiya.

Wata daya da ya gabata ne aka fara samun mamakon ruwan sama a kasar inda a yankuna da dama aka dinga samun ruwa kamar da bakin kwarya tare da tsawa.

Daraktan Hukumar Bayar da Agaji ta Kasar carlos Ivan Marquez ya ce, tun daga kamawar daminar bana zuwa yau an samu cikar koguna a yankuna da dama tare da zaftarewar kasa.

Marquez ya bayyana cewa, iyalai dubu 1,077 ambaliyar ruwan ta shafa kuma ya zuwa yanzu mutane 12 sun mutu.

Gwamnatin Kolombiya ta gargadi jama’ar kasar da su guji kusantar gabar teku, kogi ko gulbina da ke kasar sakamakon mamakon ruwan da ake samu.

 Labarai masu alaka