Kanfunan takalma sun bunkasa a Turkiyya

A cikin watani ukun farkon shekarar 2018 an bayyana cewar fitar da takalma daga Turkiyya zuwa Rasha ya karu da kaso 188 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2017.

Kungiyar Fitar Kayayyaki ta Aegean (EIB) ta bayyana cewa lamarin samarda takalma na kara habbaka a kasar Turkiyya, ganin yadda ta sayar da takalma har na dala miliyan 53 a cikin watani uku kachal ga Rasha.

Daga cikin kasashen da Turkiyya ke sayarwa takalma sun hada da Rasha, a cikin watani ukun farkon 2017 ta sayar mata da takalma na dala milyan 18.4, a yayinda a shekarar 2018 ya karu da kaso 188 cikin dari zunzurutun cinikin kuwa ya habaka zuwa dala miliyan 53.

Shugaban lamurkan fatun Aegean Jak Galiko ya bayyana cewar a shekarar 2002 sashen takalman Turkiyya ta fitar da kayayyaki na dala miliyan 131 a yayinda a shekarar 2017 ya karu zuwa miliyan 769.

 Labarai masu alaka