Saudiyya za ta sayi jiragen ruwa na yaki daga hannun Spaniya

A yayin ziyarar da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Muhammad bin Salman ya kai Spaniya ya sanya hannu kan yarjejniyar sayen jiragen ruwa na yaki guda 5.

A karon farko Sarki Felipe na Spaniya ya karbi bakuncin Yarima Salman, daga baya kuma ya yi ganawar sirri da Firaministan Kasar Mariano Rajoy da Ministar Tsaro Maria Dolores Cospedal.

Sanarwar da aka fitar daga Fadar Firaministan Spaniya ta ce, a yayin ziyarar an sanya hannu kan yarjeniyoyi da suka shafi tsaro, kayan sufurin jiragen sama, kimiyya, raya al’adu da samar da aiyuka.

Kamfanin dillancin labarai na EFE ya rawaito cewa, kudaden jiragen ruwan na yaki samfurin Avante 2200 da Saudiyya za ta saya daga hannun Spaniya sun kai Yuro biliyan 2.

Kafin ziyartar Spaniya bin Salman ya ziyarci Kasashen Faransa, Amurka, Ingila da Masar.Labarai masu alaka