Koriya ta Arewa ta sake kada hantar cikin Amurka

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Arewa Choe Son-hui ya bayyana cewa, za su sake tunani game da batun tattaunawar da aka shirya Shugaban Amurka Donald Trump zai yi na Kim Jong-un a ranar 12 ga watan Yuni.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa KCNA ya bayyana cewa, Choe na mayar da martani ne ga kalaman Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Mike Pence na cewa, Koriya ta Arewa za ta iya zama kamar Libiya.

Choe ya ce, tabbar Pence bai fahimci halin da Koriya ta Arewa ta ke ciki ba.

Ya ce, ba za su taba yin wargi ko wala-wala da ganawar da suka shirya yi ba amma batun Koriya ta Arewa ta zauna da tattaunawar ko ta dakatar da sarrafa Nukiliya ya ta'allaka ga halayyar Amurka.

Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Mike Pence ya yi wani kalami inda ya ce, idan Koriya ta Arewa ba ta cimma yarjejeniya da Amurka ba kan Nukiliya to kasar za ta zama kama Libiya.Labarai masu alaka