Angola ta kori jakadanta da ya halarci bikin bude ofishin jakadancin Amurka a Kudus

Gwamnatin Angola ta kori jakadanta da ya halarci bikin bude ofishin jakadancin Amurka a Kudus tare da daraktan gabas ta tsakiya da ya ba shi umarni.

Kamfanin dillancin labarai na Angola ya sanar da cewa, Ministan Harkokin Wajen Kasar Manuel Aygusto ya kori jakadansu na Tel Aviv Joao Diogo Fortunato da wanda ya ba shi umarnin halartar bikin bude ofish,n jakadancin Amurka a Kudus Joaquim do Espirito Santo.

Ma'aikatar Harkokin Wajen ta sanar da cewa, an kori jami'an diplomasiyyar 2 ne saboda sun aikata abinda ya bata wa kasar suna a duniya.

Jaridun Angola sun ce, korar mutanen ta biyo bayan bayar da umarni da kuma halartar bikin bud ofishin jakadancin Amurka a Kudus.

Tag: Kudus , Kora , Angola

Labarai masu alaka