Saudiyya ta lalata makami mai linzami da ‘yan ta’adda suka harba mata daga Yaman

Saudiyya ta lalata makami mai linzami da ‘yan ta’addar Houthi ‘yan Shi’a na kasar Yaman suka harba zuwa garin Najran na Kasar.

Tashar Al-Akhbariyya ta Saudiyya ta bayyana cewa, an yi amfani da garkuwar makamai masu linzami wajen harbo makamin tun kafin ya fado kasa.

Labaran da tashar Al-Misira mallakar ‘yan ta’addar na Houthi kuma ta bayyana cewa, sun harba makami mai linzami zuwa Najran daga cibiyar lantarki ta harba makamin.

A cikin kwanaki 5 da suka gabata Houthi sun harba makamai masu linzami 6 zuwa Saudiyya

Tun shekarar 2014 ne mayakan Houthi suka kwace wasu biranen Yaman da suka hada da San'a Babban Birnin Kasar inda suka yi kokarin kifar da gwamnati.

A watan Maris din shekarar 2015 kuma Saudiyya ta jagoranci Ƙasashen Larabawa wajen kai wa Houthi hare-hare ta sama a Yaman.

 Labarai masu alaka