"Ya ku 'yan siyasa ku daina kalaman kiyayya"

Shugaban kasar Sloveniya Borut Pahor ya rushe majalisar kasar a inda ya bayyana 3 ga watan Yuni a matsayar sabuwar ranar da za'a gudanar da zabe.

"Ya ku 'yan siyasa ku daina kalaman kiyayya"

Shugaban kasar Sloveniya Borut Pahor ya rushe majalisar kasar a inda ya bayyana 3 ga watan Yuni a matsayar sabuwar ranar da za'a gudanar da zabe.

Pahor, ya rataba hannu akan rushe majalisar kasar gabanin gudanar da sabuwar zabe kamar yadda doka ta tanada.

Pahor,  ya yi kira ga 'yan siyasa da wakilan jam'iyyu kasar da su guji "Maganganun kiyayya" da ka iya haifar da jidali a kasar, inda ya ja hankalin 'yan siyasa da su dunga kalamai masu inganci a yayin yakin neman zabe.

Matakin aiyanar da sabuwar zaben ya biyu bayan murabus din firaministan kasar Miro Cerar bayan kotun kolin kasar ta soke zaben raba gardamar da aka gudanar akan aikin hanyar jirgin kasar Koper-Divaca da mafi yawan al'umar kasar suka zaba.

 Labarai masu alaka