Shugabannin Amurka, lngila da Faransa sun gana bayan ƙaddamar da hari akan gwamnatin Asad

Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron ya gana da takwarorinsa na Amurka Donald Trump da ta lngila Theresa May ta wayar tarho inda ya nuna farin cikinsa akan nasarar harin da suka kaiwa gwamnatin Asad sakamakon kaiwa farar hula hari da makamai masu guba.

Shugabannin uku sun tattauna akan ci gaba da matakan kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya akan samar da zaman lafiya ta hanyar lumana mai ɗorewa a Siriya.

A ɗayan barayin kuma a ganawar manema labarai da hafsan sojojin Faransa François Lecointre ya yi da ministan tsaron ƙasar Florence Parley sun bayyana cewar harin da aka kaiwa gwamnatin Asad zai kangeta daga yin makamai masu guba da kuma baiwa farar hula damar ci gaba da lamurkan su na yau da kullum.Labarai masu alaka