Turkiyya ta gargadi Girka game da rikici a tekun Aegean

Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Girka Alexis Tsipras inda ya ce, akwai bukatar su dauki matakan kare afkuwar rikici a tsakaninsu a tekun Aegean.

Yildirim ya shaidawa Tsipras cewa, Turkiyya ta damu game da tayar da jijiyar wuya a tekun, a saboda haka ya zama wajibi Girka ta dauki matakin hana afkuwar rikici a yankin.

Ya ce, tekun Aegean ya kamata ya zama na kawance da abota, kuma idan Girka ta nisancı tayar da zaune tsaye to hakan zai amfani kasashen 2.Labarai masu alaka