Tunisiya ta yi watsi da bukatar Rundunar Tsaro ta NATO na gina sansanin soji a kasar

Tunisiya ta ki karbar Yro miliyan 300 inda ta yi watsi da bukatar da Rundunar Tsaro ta NATO ta mika mata na kafa sansani tare da zaman kwararrunta na dindin a kasar.

Ministan Tsaron Tunisiya Abdulkarim Al-Zubaidi ya yi jawabi a Majalisar Dokokin Kasar inda ya ce, an watsi tare da kin karbar kyautar Yuro miliyan 300 da NATO ta bayar a matsayin kudin goro don ba wa dakarun NATO na musamman damar zama a Tunisiya a wani bangare na yaki da ta'addanci da tsaron kan iyakoki da Tunisiyan ke yi.

Zubaidi ya ce, suna ci gaba da aiyukan kafa sansanoninsu na hadin gwiwa, kuma suna da manufar hafa gwiwa da sojojin don samar da tsaro a sama, ruwa da kasa da kuma dukkan iyakokinsu.

Ministan ya ce, sun bukaci NATO ta ba su kudin amma ba tare da sharadin lallai sai wani soja daga kasar waje ya je kasarsu ba.

Ministan ya yi nuni da cewa, har yanzu iyakokin Kasar da Aljeriya da Libiya na karkashin barazanar 'Yan ta'adda, kuma 'yan ta'addar na cin karanesu babu babbaka a yankunan Kassarin, Kaf da Jandube.Labarai masu alaka