Shugaba Erdoğan ya tattauna da Sarki Salman ta wayar tarho

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya tattauna ta wayar tarho da Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ında suka yi musayar bayanai game da kasar Siriya.

Majiyoyin Fadar Shugaban Kasar Turkiyya sun ce, Erdogan ya bayyana wa Salman batutuwa kan hare-haren Reshen Zaitun da Turkiyya ke kai wa a arewacin Siriya don yakar 'yan ta'adda.

Erdoğan ya ce, al'umar Kurdawa, Turkmen da Larabawa da 'yan ta'adda suka kora daga garuruwansu a Afrin na goyon bayan hare-haren, kuma bayan an gama za su samu damar koma wa gidajensu. 

Erdogan da Salman sun amince kan amfani da hanyoyin siyasa don warware rikicin Siriya, tare da girmama kasar baki daya.

Sarkin Salman ya nuna bukatar da ke akwai na aikin da sakamakon tarukan Geneva, Soci da Astana.

Shugabannin sun amince kan cewa, ziyarar da Yariman Saudiyya Muhammad bin Salman zai kai Turkiyya a nan gaba za ta karfafa alakar kasashen 2.Labarai masu alaka