Rasha ta bayyana sabon jakadanta da zai yi aiki a Ankara

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da kudirin dokar da ya bayyana sunan Aleksey Yerhov a matsayin jakadan Rasha a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.

Yerhov zai maye gurbin Andrey KArlok da aka yi wa kisan gilla a watan Disamban shekarar 2016.

Yerhov ya kasance tsohon konsol janar na Rasha da ke Istanbul kuma shi ne shugaban sashen warware rikici na ma'aikatar harkokin wajen Rasha.

Watanni 6 kenan bayan kashe Karlov ba tare da Rasha ta nada sabon jakada a Turkiyya ba.Labarai masu alaka