Shugaban kasar Turkiyya da na Faransa sun gana da sarkin Qatar ta wayar Tangaraho

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan dana Faransa Emmanuel Macron sun gana da sarkin Qatar Sheik Temin bin Hamed Al-Sani ta tangaraho akan rigingimun kasashen gulf da kasar ta Qatar .

Kamar yadda majiya daga fadar shugaban kasar Turkiyya ta sanar, shugabannin sun tattauna akan irin yadda yazu magance rikicin yankin na Gulf, a yayinda suka amince da cewa akwai bukatar kawo karshen rikicin yankin. 

Shugabanni sunyi amanna da wrware rikicin yankin ta hanyar lumana da diflomasi shine mafi sauki ba ta hanyar saka takunkumi ba. Haka zalika sun sha alwashin bada gudumowa yin hakkan.

Shugabannin da suka bayyana cewa ya kamata a kalubalanci dukkan nau'in ta'addanci, shun ja hankalin cewa akwai bukata kiran ko wani irin 'yan ta'adda da sunan ta'addanci ba tare da sauyiba.

Shugabannin sun kuma amince da cewa zasu dunga tuntubar juna akan al'amurran da suka shafi yankunansu akai akai.

 Labarai masu alaka