WANNE IRIN KUNDIN TSARIN MULKI ZA A SAMAR A SIRIYA?

A kan wannan batu za mu kawo muku Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana.

WANNE IRIN KUNDIN TSARIN MULKI ZA A SAMAR A SIRIYA?

Matsalolin Kasashen Duniya: 15

Daya daga cikin dalilan da ke sanya a kasa magance yaki shi ne, kasa cimma yarjejeniya bayan gama yakin. Mayar da hankali kan daukar matakai bayan kammala yaki daya daga cikin muhimman hanyoyin kawo karshen yaki ne.

A yau kafafan yada labarai na bayar da cewa, Rasha ta samar da Kundin Tsarin Mulki ga Siriya kuma sun amince da Amurka kan hakan. Makomar Siriya, a ce wai wadannan maynyan kasashe ne za su samar da ita to ai hakan ba shi da amfani ga al’uma da kasashen da ke yankin. Shin Kundin Tsarin Mulki da Manyan Kasashe suka ba wa kansu damarmaki a cikinsa zai kawo zaman lafiya ga yankinmu? Sakamakon haka ya ci a ce sun dauki kungiyoyin fafutuka dakwararru masu zurfin tunani na kasashen yankin.

Duk kundin tsarin mulki da aka samarwa wata al’uma ba tare da duba izuwa ga tarihi, al’ada, imani da dabi’unta da yanayin rayuwarta ba to tabbas ba zai kawo mata zaman lafiya ba. Ba zai warware matsalolin ba. Bangarorin sabon kundin tsarin mulkin da aka bayar da shawara a ba wa Siriya zai iya zama abin misali a kan wasu kasashen daban.

Kundin tsarin mulki da zai ba wa masu rinjaye damar jogarantar kasa: Idan aka kalli gwamnatocin Gabas ta Tsakiya, za a ga cewa babbar matsalar gwamnatocin ita ce ta yadda ‘yan kasar mafiya rinjaye ba su suke rike da akalar mulkin kasashen ba. Kasashen da shugabanninsu ba su da rinjaye to suna amfani da sojoji da ‘yan sanda da ma nuna bukatar taimakon wasu kasashen waje don yin jagoranci tare da durkusar da jama’ar kasar. A saboda haka kundin tsarin mulki da zai samu karfi daga al’uma tare da ba wa mafiya rinjaye damar yin mulki shi ya kamata a samar. Kundin tsarin mulki da bai yi biris da masu rinjaye ba ne wanda zai amfani al’uma. Ta haka ne wata kasa za ta iya karfi a ciki da wajenta.

Kundin tsarin mulki da ya takaita wa’adi don samar da sauyin hannu: Babbar matsalar rashin karfin kasashen Gabas ta Tsakiya shi ne yadda kundin tsarin mulki bai bayar da damar sauya hannu ba. Sarakai da shugabannin da suka hau mulki suna kasance wa har sai bayan sun mutu. Wannan yanayi ne mai haifar da matsaloli aa wadannan kasashe. Da farko wannan abu na sanya shugabannin su rasa iko kan jama’arsu. A lokacin da shugabannin suka ga sun kasa samun iko kan jama’arsu sai su fara neman taimako daga kasashen waje. Haka su ma ‘yan adawa da suke kasar wadanda ba su yadda da wannan tsarin ba sai su fara neman taimako daga manyan kasashyen waje. Idan ana son kar a samu irin wannan abu to dole da gwamnati da ‘Yan adawa su samar da tsari da kansu wanda zai takaita wa’adin mulkin shugaba. Tsarin zango 2 da ba zai wuce shekaru 10 ba a kasashen Gabas ta Tsakiya zai magance matsaloli da dama tare da samar da zaman lafiya.

Kundin tsarin mulki mai kare martabar bambance-bambance: a lokacin da kundin tsarin mulki ya bayar da damar shugabanci ga bangare mai rinjaye a wata kasa, to zai kuma kare martaba, ra’ayi, Addini da martabar ‘yan tsiraru ko marasa rinjaye. Batun hakkokin mutane bai shafi a ce na masu rinjaye ko marasa rinjaye ba ne.

Kundin tsarin mulki mai bayar da dama ga gwamnati daya: Tsari da zubi na kafa yankuna masu cin gashin kansu ba zai, samar da zaman lafiya a Siriya ba. Iraki da Spaniya ne misali na karara da z aa iya bayarwa kan wannan batu. Idan aka samar da wannan tsari a Siriya, to wani bangaren zai yi kokarin samun iko fiye da yadda ya kamata, wanda hakan zai sanya kasashen waje ci gaba da tsoma baki a harkokin mulkin kasar. Wannan tsariba ya samar da zaman lafiya ga kwanciyar hankali ga al’umar da ke cikin rikici da zullumi. Idan da za a ce a dakatar da yaki to da wannan tsarin zai yi amfani. Amma domin samar da zaman lafiya dauwamamme, kare bartabatar bambancin da ke tsakanin al’Umu, samar da garantin hakkoki da ‘yanci na samu wa ne a lokcin dakaka bayar da karfi da cikakken iko ga gwamnati daya ta kasa da kanana hukumomi a cikin kasa.

Kundin tsarin mulki mai samar da adalci a wakilci, zaman lafiya a shugabanci da bayar da damar zartarwa ga gida daya: A lokacin da kundin tsarin mulki ke bayar da damar wakilcin al’uma a majaisar dokoki, to dole ne kuma ya bayar da cikakken karfin jagorancin kasa ga wani bangaren. Idan tsari mai amfani da majalisar dokoki zai bayar, to damarmakin shugaban kasa za su zama na je ka na yi ka ne. Idan aka ce a kasa an samu Firaminista da Shugaban Kasa masu krfin iko to ba a samun damar shugabanci cikin zaman lafiya da daidaito. Hakan na ba wa kasashen waje damar tsoma baki a harkokin mulkin irin wadannan kasashe.

Kundin tsarin mulki mai kare martaba da dabi’un al’uma: Dabi’a mafi daraja a Gabas ta Tsakiya ita ce Addini. İdan aka dauki ra’ayoyi daya kan bayyana makomar Addini da Daula to hakan watakila ba zai kawo mana waraka ba. Kasashen yammacin duniya da suke rada gwamnati da Addini da suka jefa dan adama a matsala a lokacin yakin duniua na I da na II, sun kasance abokan wasu shugabannin kasashen Larabawa da suka ce, Saddam da Gaddafi na shugabanci da tsarin Shari’a wanda abin ba haka ba ne. A saboda haka kowacce kasa za ta kalli tarihinta da dabi’unta na zamantakewa wajen bayyana matsayin Addini a harkokin jagoranci da shugabanci. A Gabas ta Tsakiya, kasashe na aiki ne ta yadda suka san suna da tsarin jagoranci tun daular da ta gabata kuma haka a tsarin shugabanci. Tsari ne d ya bayar da ‘Yanci ga kowa. Amma a Siriya an samar da kundin tsarin mulki da ya yi biris da Addini. Ta haka an sake shiga yanayin da ba a ba wa jama’a dama a hannunsu ba inda Gabas ta Tsakiya za ta sake koma wa cikin halinta irin na yau.

A lokacin da kundin tsarin mulki ya ke bayani kan Addini to dole ya bayar da cikakkiyar dama ga masu rinjaye. Kamar yadda ya ke a Saudiyya da Iran bai kamata ya mayar da hankali kan Addin, daya ba kawai.

Kundin tsarin mulki da zai amince da daidaiku ba wai jama’aun mutane ba: A Gabas ta Tsakiya ana da mabiya Addinai daban-daban, al’uma kala-kala, masu mabambantan tunani, kuma suke da kabilu da dangi daban. Idan aka ce a yanki irin wannan za a samar da kundin tsarin mulki na bai daya wajen bayyana al’uma, to kamar yadda aka gani a Bosniya za a shiga rikici na siyasa. Samar da kundin tsarin mulki na bai daya kan al’uma na daskarar da ita. A saboda haka dole kundin tsarin mulki ya zama mai amince wa da daidaikun mutane da asalinsu. Mutane za su iya haduwa waje guda su yi komai ton tabbatar da kansu a kasa.

Babu wani yaki da za a yi ta yin sa har abadal abidin. Duk karfin wasu kasashe a lokacin da ake yak, to bayan yakin tabbas za su rasa wannan karfin ikon. Za a yi kuskure wajen assasa kasar Siriya bayan yaki wadda za ta samar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu. A saboda haka dole tın yanzu a fara aikin samar da Siriya mai ‘yanci da amince da hakkokin djama’a da ba su damarmaki domin hakan ne zai kawo wa yankinmu zaman lafiya madauwami. Amma in ba haka ba to manyan kasashen nan dai za su sake nasara bayan an gama yakin

Sharhin da Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazit Farfesa Kudret Bulbul ya yi mana kenan.Labarai masu alaka