Matsalar yawan harbe dalibai a makarantun Amurka

Daga shekarar 1975 zuwa yau ana fadar cewa, an kashe mutum miliyan 1.5 sakamakon harbi da bindiga a Amurka, wannan adadi ya fi wanda Kasar ta ke rasa wa a wajen yaki.

Matsalar yawan harbe dalibai a makarantun Amurka

Matsalolin Kasashen Duniya: 13

Kamar kowanne mako, a wannan makon ma za mu kawo muku sharhin Farfesa Kudret Bulbul shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit wanda ya yi kan kisa da ake yi a makarantun Amurka.

Kisa a makarantun Amurka

Wadansu layuka ne na mutane da suke tattaki suka fara daga garuruwan Amurka tare da fada zuwa wasu yankunan, ana ganin wannan guguwa na kadawa tana shiga wasu kasashen. “Ku yi tafiya saboda rayuwarmu” shi ne taken taron da matasa suka saka yi a birnin Washington a ranar Asabar din da ta gabata inda suka mayar da martani kan yawan hari da ake kai musu makarantu tare da kashe dalibai. Kusan matasa dubu 500 ne suka halarci taron. Wani karamin dalibi ya daga allo da aka rubuta cewa “Ni ko dakakkiyar gyada ba zan kawo makaranta ba. A'a ga makamai.”

Kashe-Kashe a makarantu

Kashe-Kashe a makarantu a makarantu a Amurka na kara yawaita fiye da hankali. Yara, iyaye da duk masu hankali na nuna martani ga wannan ta’asa inda suke naman a dauki matakan kariya. A karo na karshe a watan Fabrairun 2018 an kai hari wata makaranta tare da kashe dalibai 17. A shekarar 2012 an kashe dalibai 26 a Conneticut a 2007 kuma an kashe 32 a Virginia.

A kowacce shekara dubunnan dalibai ake kashe wa da bindigu a Amurka. A kowcce rana ana kashe dalibai 5 zuwa 19 wanda za a iya samun bayanan haka a yanar gizo. Wannan kisa na dalibai a Amurka ya ninka na sauran kasashen duniya.

Kisan Mutane gama-gari

Kashe mutane a makarantun Amurka, ya zama wani karamin abu da ya fito daga kisan da ake y a kasar baki daya. A dukkan bangarori 4 ana kisan gilla. Akwai hari da bindigu da arangama, hatsari wajen harba bindiga da kashe jama’a da dama a lokaci guda. A Amurka a kowacce rana mutane 92 ne suke mutuwa sakamakon harbin bindiga. Daga shekarar 1975 zuwa yau ana fadar cewa, an kashe mutum miliyan 1.5 sakamakon harbi da bindiga a Amurka, wannan adadi ya fi wanda Kasar ta ke rasa wa a wajen yaki. A shekarar 2017 an kashe mutane 58 a Nevada, a Florida a shekarar 2016 an kashe 49.

Kisan mutane daya-daya na bayyanuwa ne bayan dan bindiga ya bayyana kansa. Adadinmutanen Amurka ya kai kaso 4.4 na al’umar duniya amma su suke da kaso 42 na makaman da ke hannun daidaikun mutane a duniya. Kaso 31 na kisan mutane da yawa da ake yana afkuwa ne a Amurka. Bayan Amurka Kasar Yaman ce ke niye mata baya wajen mallakar makamai ga daidaikun mutane.

Yawan aikata manyan laifuka

Bisa ga alkaluman duniya, yawan aikata manyan laifuka a Amurka na da yawa sosai. Alkaluman Hukumar Bincike ta Tarayya (FBI) na cewa, a shekarar 2016 a Amurka an aikata manyan laifuka miliyan 1, da dubu 195 da dari 704. AN kashe mutane dubu 15,696. Kaso 71 na wadannan kisa an yi su ne da bindigu. Adadin mutanen da ‘yan sana suka kashe a shekarar 2016 sun kai dubu 1,152. A Amurka ne aka fi kowacce kasa yawan yin fyade. Kaso 62 na wadanda ake wa fyade suna da shekaru 18 zuwa sama inda kaso 11 kuma ‘yan shekaru kasa da 11 ne.  

Laifuka ne da ke cin karo da ‘yanci?

Ko da a ce kafafan yada labarai ba sa gani, to laifukan na da yawa sosai. Amma mu batunmu shi ne na kisa a makarantu. Bari mu dawo kan wannan batu. Idan aka kalli batun kisa a makarantu a Amurka, to ana yi ne game da yadda kundi tsarin mulki ya ba wa jama’a damar mallakar makamai. Mallakar makamai na daya daga cikin ‘yancin da kundin tsarin mulkin Amurka ya ba wa ‘yan kasar.  Amurka kasa ce da ke cike da rikici. Sakamakon haka ake ta muhawara a wannan kasa game da batun dauka ko mallakar makamai. Yadda kawai ake mayar da hankali kan batun ‘yanci da kundin tsarin mulkin ya bayar, ba batu ne da wadanda ba sa cikin Amurka suka fahimta ba. Akwai bangarorin muhawarar da dama. A ce a ksar da ake kashe dubunnan mutane kowacce shekara ana mayar da hankali kan ‘yancin da kundin tsarin mulki ya bayar ba abu ne mai kyau ba, hakan wasan yara ne. A tare da hakan, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da shawara gurguwa mai ban mamaki, ya ce, a ba wa malamai makamai su ma. Haka kuma majalisar dokokin Florida ta amince da wannan abu. A kasar da ake kashe dubunnan daliba wanda kowa yana da tasa bindigar, sannan a ce za a kara wa malamai wasu ta yaya za a warware matsalar? Shin ba wa malamai bindiga ne zai kare daliban? İdan dalibai suka mallaki manyan bindigu,to su malaman Nukiliya za a ba su? Yadda Amurka ke bayar da makamai a wasu kasashe haka ta ke so ta yi a tsakanin malaman makaranta da dalibai? Kamar dai abin bai yiwu ba.

Me ya kamata a yi?

Kamar yadda Marubuci dan kasar Spaniya, Ortega Gasset ya ce, wayewar kudi cewa, akwai matsala ne. A yayinda cigaba ya habaka sai hatsari ya girmama. Mhawara kan kashe mutane na bukatar a ta’allaka ta ga ‘yancin da kundin tsarin mulki ya bayar. Amma baya ga wannan akwai batutuwa da dama da suka shafi lamarin. A wasu lokutan a shafun yanar gizo ake yadda me mai yin kisa ya zai yi, ya zai yi da yaya ake yi. Akwai bukatar nazari kan wannan abu. Game da hakan kamlaman marubuci ba’amurke Adam Lankford  suke da muhimmanci. Lankford ya ce, kisan mutane da dama a Amurka a lokaci guda, na haifuwa ne daga al’adar kasar na mallakar bindigu da yadda daliban suke yin yadda suke so.musamman a cikin iyali da ake da matasa da suke ganinnkansu a matsayin na zamani. Ba za a tsaya tattauna batun kisan mutane a Amurka ba kan hana daukar makamai ko gyara ‘yancin da kundin tsarin mulki ya bayar ba. Amurka kasa ce da kisan gilla ya kashe mutanenta fiye da yaki. Akwai bukatar bayar da ilimi, horoda tarbiyya ga Amurkawa. Me ya sa al’umar Amurka da ta fi kowacce ci gaba a duniya ta ji tana bukatar mallakar makamai? Shi wannan na da alaka da tsaron al'uma ko daidakun mutane?

Ina fata tattakin ada aka yi Amurka zai samu abinda ya ke so. Hakkin rayuwa ya fi komai daraja.

Sharihin Farfesa Kudret Bulbul shugaban tsangayar nazarinharkokin siyasa a jami’ar Yildirim Beyazit wanda ya yi kan kisa da ake yi a makarantun Amurka.

 Labarai masu alaka