Dalilan da suka haifar da matsalolin da Turai ke ciki a yau

Kallon kyamar Musulunci, nuna wariya da hantara baki da ‘yan gudun hijira a kasashen Turai a matsayin barazana, na kara rufe Turai ne tare da jefa ta ciki rikici, wanda a shirye-shiryenmu na baya mun tattauna a kai.

Dalilan da suka haifar da matsalolin da Turai ke ciki a yau

Matsalolin Kasashen Duniya-12

Jama'a barkanmu dai da kuma sake kasance wa a cikin shirin Matsalolin Kasashen Duniya.

Kamar kowanne mako, za mu kawo muku sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

A baya na kwatanta irin abubuwan da suke faru wa a Turai da irin abin da ya faru a ranar 28 ga watan Fabrairu a Turkiyya.

Alkaluman ma’aikatar harkokin wajen Jamus sun ce, a shekarar 2017 kadai an kai wa Musulmai hari sau 950 wato kusan sau 3 a kowacce rana. A yanzu an kai matsayin ya wuce wannan ma.

Shin Turai za ta iya fita daga wannan rudani da duhun?

Kafin haka dole ne a fara tsayuwa wajen duba dalilan wannan rikici.

Rashin tabbas a duniya: Amurka, Rasha, China, Turkiyya, Indiya da Latin Amurka na kalubalantar tsarin da aka dora duniya a kai bayan yakin duniya na 2. Wannan rashin tabbas ya sanya a kowacce kasa ana samun rikici. Ana tuhumar hadin kai na al2ada da nuna kyama. Sakamakon haka ya sanya ana sake kula alaka a tsaknin kasashe. A tsakanin kasashe ana samun hadin kai ko hamayya da juna.

Kafin Yamma ta hade ba ta gama nasara ba: Turai da Amurka ba su gma samun abinda suke so ba kafin a fara batun dunkulewar duniya waje guda. Kasashen irin su China, Indiya, barazil da Turkiyya sun zama wadanda suka fi amfana tare da yin nasarar a wannan lokaci na dunkulewar duniya. Sakamakon haka ya sanya wasu kasashe da suka hada da Amurka suka ki amince wa da tsarin da suka yi amfani da shi wajen nasara a baya na bayan da dama shiga kasuwanci kasashen duniya da janye haraji wadanda manufofi ne na dunklewar duniya waje guda. Akwai matsaloli da dama da suka hada da na siyasa, zamantakewa, tattalin arzik da halayyar dan adama da suka hana nahiyar samun cikakkiyar nasara a lokacin da duniya ke dunkulewa.

Maganganu, zantuttuka, da ma aiyuka na Turai na yin adawa da tsarin dunkulewar duniya waje daya. Wannan abu ne karara da ake gani a yammacin duniya. Amma kafin duniya ta dunkule waje guda an samu kasashe irin su Turkiyya da suka yi nasara da samun riba, wanda hakan ke kawo tambayar cewa, ko shugabanni a kasashen suna ci gaba da kalaman adawa da tsohon tsarin hadewar duniya waje guda.

Rashin Al’umu daban-daban a Turai a baya: Daya daga cikin dalilan da suka janyo rikici a Turai shi ne yadda aka kalli al’uma daban a matsayin daya. Al’uma daban-daban ana mata kallon daya tal. Amma a lokacin da wani bako ya zo bakin kofarsu, ko abokin aiki, ko mai bayar da aikin ka lebura sai abun ya sauya. Turai ba za ta iya jurar wannan ba saboda a baya ba ta da al’Umu da yawa da suke daban-daban da juna. A shekaru 100 da suka gabata ne kawai za a iya cewa, a Turai an samu rayuwa tsakanin al’umu daban-daban. A wajen malaman Tarihi shekaru 100 kamar jiya ne.

Shugabannin marasa tunani: Jam’iyyun dama da hagu da suke Turai, mai makon su zama suna yakar tsaurin ra’ayi da nuna wariya, sai suke goyon bayan wadannan munanan dabi’u don kar su rsa kuri’unsu. Kamar yadda wannan lamari bai durkusar da jam’iyyun Naji da na Shishanci ba, haka ya ke kara ingiza tsaurin ra’ayin jam’iyyun hagu da na dama.sakamakon haka ya sanya a Turai jam’iyyun masu tsaurin ra’ayi na samun ragamar shugabanci.

Tasirin yankunan da aka mamaye: bangarorin da aka mamaye wadanda ake fama da rikici a kasashensu suka kuma gudu Turai don fake wa, kuma suka rasa amintar zamantakewa sai suka zamanto suna samu bakin rikici da kasashen da suka je. Turai da ta goyi bayan mamaye wadannan mutane, sai ga shi kuma tana zama mai adawa da nuna kyama ga ‘yan gudun hijira da ke da ba a mamaye ba suke kuma kokarin tabatar da kawunansu. Wannan abu na kara nuna wa wadanda ba a mamaye ba yadda Turaike kara ci gaba amma irin na mai haka rijiya. Domin tana da barazana da kuma kasancewa waje na kyamar wadanda ba ‘yan asalinsa ba.

Idan za a iya bayyana matsalolin turai kamar yadda aka zayyana a sama, to z aa ga ba za a iya warware rikicin a cikin kankanin lokaci ba. Saboda wadannan dalilai na sama ba dalilai ne da za su kare ko a tafiyar da su nan da kankanin lokaci ba. A lokutan da ke fuskantar wadannan matsaloli, shugabannin da za su tari aradu da ka za su iya tafiyar da su tare da daidaita kasashensu.

A irin wannan hali masu ilimi da basira za su iya taka rawa sosai. Game da yadda Turai za ta fito daga wannan babban rikici da ta fada, shin bangaren da ke da ‘yanci kuma ya ke amince da wasu al’umu yana lura? Ba za a taba tunanin cewa, nahiyar da ta sha fama da matsalar nazi a Jamus da ta Fashisanci a Italiya a ce wai ba ta san da wannan matsala ba. Amma dai mutanen ba su a matsayin magance matsalar tare da tafiyar da rikicin. Ana tafiya ana kara rasa ‘yanci. Wadannan ba sa kallon yadda suke kuntatawa ‘yan gudun hijira da Musulmai.

Ni ba ni da sa ran cewa, wannan matsala da Turai ta fada za ta iya fita daga cikinta nan da wani dan lokaci. Ina da tunanin Turai za ta fuskanci matsaloli da dama a nan gaba saboda abubuwan da ta shuka. Zan so a magance matsalolin. Ina fatan haka a ce Turai ta fahimci matsalolinta ba tare da an gwabza yaki ba. Nan da wani lokaci ta fahimci cewa, tana fada wa wata rijiya mai duhu kan makomarta da kuma hana mutane ‘yanci da ta ke. Mu dai muna yin abin da za mu iya. Za mu ci gaba da nuna wa Turai matsalolin da ta ke da su, da kuma hanyoyin magance su.

Mun gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.Labarai masu alaka