Tasirin Yakin Canakkale ga duniya baki daya

Yakin Canakkale da irin tarinsa ga duniya: A shekarar 1915 Daular Usmaniyya ta yaki manyan Kasashen Duniya da suka so mamaye ta. An gwabza yaki a gabar tekun Canakkale (Geliboli). Ko ta yaya nasarar da Musulmai ta yi ta shafi sauran duniya?

Tasirin Yakin Canakkale ga duniya baki daya

Matsalolin Kasashen Duniya-11

Masu karatu barkanmu dai, tare da sake kasance wa a cikin shirin Matsalolin kasashen duniya. Kamar kowanne mako, a wannan makonma za mu kawo muku sharhin da shugaban tsangayar nazarin harkokin siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara FarfesaKudret Bulbul ya yi mana kan birnin Çanakkale da tasirinsa kan bil’adama a yau.

Ba za a wuce Canakkale ba, Insaniyya ba za ta fadi ba

A tarihin kaddara kasashen duniya akwai abubuwa da dama da suke faruwa. Wani lokacin wadannan abubuwa na iya sauya duniya baki daya. Yakin Canakkale da muke tuna wa da shi bayan shekaru 103 yaki ne da ya sauya fasalin duniya.

A yayin wannan yaki an kutsa kai zuwa Istanbul tare da kokarin kawar da Daular Usmaniyya inda aka so mika wa Rasha taimako. Sakamakon haka Ingila, Faransa, Ostireliya, Kanada, Niyuzelan da Indiya da ma wasu kasashen duniya manya suka aike da dakarunsu dubunnai zuwa Canakkale. Domin samun damar wuce wa ta tekun sun kai hari kan rundunar da ke wannan waje. Da suka kasa wuce wa amma a kan hanyarsu sai suka hadu da dakarun Daular Usmaniyya masu imani.

An fara yakin a watan Fabrairun 1915 kuma aka kammala a watan Disambar shekarar. An kashe dubunnan daruruwan mutane. Wasu da dama sun mata inda aka kama dubunnan a matsayin fursunonin yaki. Watakila na daya daga cikjin abubuwan tarihi masu ciwo da aka samu a doron kasa. An kone kayan yaki da dama. Sakamakon yadda a yake-yaken baya mutane da dama suka yi shahada yasanya an dibi matasa da dama a lokacin wannan yakin. Sakamakon haka ake kiran wannan yaki da na “Yan shekaru 15”. har wata waka aka yi game da masu shekaru 15 da suka je wannan yaki.

A shekarar akwai daliban Sakandire da dama da suka halarci wannan yaki. Akwai daliban Galatasaray, Izmir da ma makarantar Sakandire ta Konya da na yi wadda aka bude lokacin Sarki Abdulhamit, wadanda duk ba su gama makarantar ba suka yi Shahada a wajen yaki.

Duk da ba a samu wasu takardu ajiyayyu game da yakin ba, ana cewa, Daular Usmaniyya ta rasa sojoji dubu 250 da suka yi shahada. Wadannan sjoji mafi yawansu daliban Sakandire, Makarantun Islamiyya ko jami’a ne. yadda mutane masu ilimi suka yi Shahada ya janyo matsala sosai a gaba.

Shahidan Rundunar Sojin Daular Usmaniyya sun kasance sojojin Daular da ke cikin iyakarta ko kuma suke wa a wasu yankunan daban. Akwai Shahidai daga yankunan Turkiyya na yanzu da ma kasashen Balkan, Gabas ta Tsakiya da Caucasia.

A daidai wannan gaba ina so na bayyana abinda na ji daga Dattijon kasar Kosovo Malam Ilyasu. Ya ce, daga kauyensu akwai sojoji da dama da suka halarci yakin Canakkale. Amma bayan yakin sojoji 3 ne kawai suka yi saura. Kuma sun yi mamakin me za su fada wa sauran sojoji a lokacin da suke kan hanyar dawo wa kauyensu. Saboda a gida akwai iyaye, ‘ya’ya, mata, kanne da masoyan Shahidan na ta jiransu. Sai suka ce idan sulka shiga kauyen to za su karya zukatan mutanen da ke jiran ganin dukkan sojojin sun dawo kalau. Sakamakon haka suka yanke shawarar shiga kauyen a lokuta daban-daban kuma daya bayan daya. A lokacin da jarumina farko ya shiga, kamar yadda aka zata kowa sai tambaya ya ke yi ina wane ina wane?. Bayan sati daya sai daya sojan ma ya shiga kauyen. Shi ma sai jama’a suka yi tambayarsa ina sauran sojoji suke. Ya ce ai suna nan tafe. Haka na ukun ma ya zo har sai da jama’ar kauyen suka fitar da ran anin sojojinsu da suka yi shahada.

Asalin yakin Canakkale na da manufar yakar yunkurin ‘yan mulkin mallaka wajen mamaye yankunan Daular Usmaniyya tare da hana Azzulumai mamaye yankunan. Duk da amfani da makamai na zamani da kasashem Turawa suka yi, amma jama’ar yankunan da ake zalunta ba su ba wa 'yan mulkin mallaka damar wuce wa ba. Musulman Indiya da Afganistan ba su yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da gudunmowarsu a lokaci da bayan yakin na Canakkale. Wannan alama ce da ke kara karfafa zuciyar dan adam. A yanzu haka akwai wurare da dama da suke ci gaba da mamaya a dun,ya. Al’umar da ake zalunta sun hada kai a Canakkale tare da yakai azzalumai inda suka kubutar da kawunansu.

Duk wani irin yunkuri na yakar ‘yan mulkin mulkin mallaka na da daraja. Kuma ta yaya za a yi haka, ta wacce siga da dabara da kuma wadanne irin kalamai za a fada abu ne mai muhimmanci. A lokacin da ‘yan mulkin mallaka ke zalunci a yau muna ganin yadda ake amfamni da kalaman nuna wariya da tsana. Karfi ne ga mutanen da ake mamaya da kar su yi amfani da irin wadannan kalamai wajen yakar masu mamaye su. Abubuwan da suka faru a lokacin yakin canakkale da bayan sun isa su nusar da mu.

Kasashen Ostireliya da Niyuzelan da ba su saba yaki ba sun kusanci Canakkale da manufar samar da wata al’uma. In haka ne mu al’uma ce da ba mu taba samar da wata al’uma ba sakamakon nasarar yaki da muka yi. Mu al’Uma ce da ba ma kallon wasu a matsayin daban da mu. Canakkale ma haka ya zama. Haka al’umarmu ta ke, kuma kalaman da Ataturk ya yi na kara taikace wannan batu.

Samar da kalaman nuna kyama ga masu mulkin mallaka, zai sake kaskantar da mu ne kawai tare da rufe kofofinmu. Hakika yana da wahala. Amma duk ta yadda wadannan hare-hare za su shafi darajarmu da wayewarmu, muna sa ran yakar mamayar ‘yan mulkin mallaka. Ko da ‘yan mulkin mallaka sun nasara na wani dan lokaci, to idan muka yi amfani da hanya mai kyau da ba rufaffiya ba, wadda ba ta nuna wariya, to za a magance azzalumai. Kuma duk wasu masu mulkin mallaka da kaka gida za su fadi kasa warwars.

Mun kawo muku sharihin shugaban tsangayar nazarin harkokin siyasa na Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul. Labarai masu alaka