Gwamnatin Asad ta mayar da Gabashin Guta yankin kissar bayin Allah

Tun daga shekarar 2013 kawo yanzu yankin gabashin Guta da ya hada da Damascus da Jobar, musanaman yankunan da ‘yan adawa suke a gabashin Siriya, sun kasance karkashin kangewar gwamnatin Asad da magoya bayansa

Gwamnatin Asad ta mayar da Gabashin Guta yankin kissar bayin Allah

Tun daga shekarar 2013 kawo yanzu yankin gabashin Guta da ya hada da Damascus da Jobar, musanaman yankunan da ‘yan adawa suke a gabashin Siriya, sun kasance karkashin kangewar gwamnatin Asad da magoya bayansa. A gabashin Guta gwamnatin Asad da magoyabayansa da kuma Rasha sun aiyanar da ruwan bama-bamai ta sama a cikin ‘yan kwanakin nan. A sanadiyar kashe mutun 250 a cikin kwanaki uku ne ya sanya kwamitin tsaron MDD gudanar da taron gaggawa inda aka amince da a tsagaita wuta a Siriya. Sai dai wannan matakin kwamitin tsaron MDD a gabashin Guta na nuni ga ci gaban kisan bayin Allah a yankin ne kawai. Saboda ana ci gaba da kai hare-hare a asibitoci da kuma guraren samar da abinci a yankin, lamarin dake nuni ga irin mawuyacin halin da mutanen yankin ke ciki.

Akan wannan maudu’in mun kasance tare da Mal. Yazar Can ACUN dake cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki watau SETA dake nan Turkiyya.

A sanadiyar yarjejeniyar Astana an kafa yunkunan kula da samar da zaman lafiya guda uku a yankin İdlib da Rundunar Sojan Turkiyya za ta ci gaba da kula dasu a bisa ka’idar samar da yankunan lumana. Sai dai yankunan Guta, Humus da Dera da suka kamata su kasance karkashin kulawar rundunar sojan Turkiyya basu kasance a hanunta ba. Gwamnatin Asad da magoyabayanta sun karkata alkalumarsu zuwa Guta inda suka dinga kaiwa farar hula hari baji ba gani.

Kafin ma fara kai hare-hare ta kasa, rundunar sojar Rasha ta aiyanar da hare-haren bama-bamai a yankin ta sama. Sojojin Rasha da na gwamnatin Asad ba tare da ware farar hula daga soja ba sun gudanar da irin wadanan hare-haren halakar da farar hula a yankin Halep. Akan faruwar irin wannan ne a gabashin Guta kwamitin tsaron MDD ta gudanar da taro na musanman, inda  ta sanar da yunkurin tsagaita wuta a Siriya. Sai dai kasancewar matakin tsagaita wutar ba zai iya shafar kungiyar DAESH da Al-Kaida ba ya karya gabar yunkurin gaba daya.

Hakika, Rasha ta kasance tana kalubalantar kungiyoyin ta’addar DAESH da Al-Kaida ne kawai a rubuce, amma a gaskiyar lamari masana ‘yan adawa na Rasha na gudanar da harin bama-bamai ba tare da kulawa da farar hula ba a yankin. Hakan na faruwa ne saboda kwamitin tsaron MDD ba ta bayyana wa ta takurawa ko hukunci ga wadanda za su iya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta Siriya ba, lamarin da ya sanya rashin amincin matakin gaba daya.

Fitinun da kungiyar Ahrar Ash Sham ta Rasha da kungiyar Jays Al-Islam suke yi a tsakaninsu a gabashin Guta na karantar da cewa basu da alamun bin umurnin matakin na kwamitin tsaron MDD akan tsagaita wuta. A sanadiyar fada tsakanin kungiyoyin biyu an kama da yawan mambobin Jays Al Islama, inda sanarwar Ahrar ush Saham ta Rasha ke nuna cewar ta aiyanar da hare hare da dama domin kalubalantar kungiyar Jays Al Islama a yankin Idlib

          A karara dai hare-haren da Rasha da gwamnatin Asad suke yi basu kasance ba facce kisar gilla a gabashin Guta. Kange gabashin Guta mai dinbin al’umma bai karantar da komai facce matakan kashe daruruwan al’umar yankin daya bayan daya.

               Rasha ta kasance tana nuna kyakyawar niyar ta a munafunce ga matakin kwamitin tsaron MDD na tsagaita wuta inda take yadawa a tsakanin karfe tara zuwa biyu agogan Guta da cewa an tsagaita wuta amma gwamnatin Asad da magoyabayanta tun ranar da aka bayyana tsagaita wutar kawo yanzu basu bar kai hare hare ba a gabashin Guta. Duk da dai sun aminta da cewa a tsagaita wutar tsakanin 9-2 agogon Rasha, sojojin Asad na kai hari a Guta da karfe 9.30 a garuruwan gabashin Guta da suka hada da Duma, Beyt Sava da Merc inda farar hula da dama suke zama.

                  Turkiyya wacce daya daga cikin kasashen lumana uku ne, tana iya kokarinta ta amfani da yarjejeniyar Astana domin kawo karshen rikicin gabashin Guta. Domin bin hanyoyin yarjejeniyar Astana zai fi kawo karshen hare-haren da gwamnatin Asad da Rasha keyi a Guta fiye da matakan kwamitin tsaron MDD. A dai-dai lokacin da take ci gaba da yunkurin bin ka’idar Astana domin warware matsalolin Guta tana kuma neman hanyar isa gabashin Guta domin baiwa al’umar yankin tallafi da kuma warkar da wadanda suka raunana.

Wannan rikicin na gabashin Guta bai kasance ba facce kara rikitar da kasar ta Siriya, matsayar Rasha da gwamnatin Asad a Siriya bazai iya warwaruwa ta hanyar matakan MDD ba, sabili da kasashen din-din dim din MDD biyar, amaimakon samar da zaman lafiya basu kasance ba facce aiyanar da lamurkan biyan bukatunsu. A yau dai kila a dan samu tsagaita kisar farar hula na dan lokaci a Guta ko kuma dukkan matakan su zama marasa tasiri. Hakika, matukar MDD bata canja tsarinta ba , babu ko shakka ba za ta iya  warware matsaloli irin na gabashin Guta a fadin duniya ba.

 

Wannan sharhin Mal. Yazar Can ACUN ne dake cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki watau SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

 Labarai masu alaka