Gurguwar Dabarar Amurka

Kimanin sati biyu da suka gabata ne wasu jami’an gwamnatin Amurka suka ziyarci Turkiyya domin tattauna da shugabanin Turkiyya.

Gurguwar Dabarar Amurka

Kimanin sati biyu da suka gabata ne wasu jami’an gwamnatin Amurka suka ziyarci Turkiyya domin tattauna da shugabanin Turkiyya. A tataunawar da akayi na tsawon lokaci, anyi nasarar yanke hukunci daukar matakan warware matsalar musayar bayanai ne tsakanin kasashen biyu.

Bayan hakan, abinda aka dauki mataki akai kuma shi ne, lamarin da aka kwashe shekaru hudu ana fama dashi, lamarin da ya sanya gwamnatin Turkiyya sukar Amurka akan dangantakarta da kungiyar ta’addar PYD/PKK, haka kuma alkalan kasar Amurka ma a ko wacce rana na sukar dangantakar Amurkan da wadannan kungiyoyu wadanda a Amurkan ma an bayyana su a matsayar ‘yan “ta’adda”

Da yawan hukumomin Amurka da suka hada da kungiyar leken asirin CIA sun tabbatar da cewa PYD wa ta barayin PKK ce. Amma mai magana da yawun Amurka da sauran mukarabai kan fusata duk lokacin da Turkiyya ta soki alakar Amurka da kungiyar PYD/PKK da cewa tana kokorin karya manufar Amurka a yankin. Bayan haka kuma su dinga zargin kafafen yada labaran Turkiyya ko wasu da laifin da suke aikatawa.

Kungiyar PYD/PKK Kalubalece ga ‘Yancin Yankunan Turkiyya

Amurka ta yanke hukuncin soma fara dangantaka da kungiyar PYD/PKK ne a shekarar 2014. A lokacin da kungiyar DAESH ke aikata ta’asa a yankunan Rojava, a arewacin Siriya dake da makwabtaka da Turkiyya, a lokacin da Turkiyya tabar kungiyar da gwamnatin Kurdawan arewacin Iraqi ta karfafa ta kuma basu damar shiga yankunan Rojava.

Abin da gwamnatin Obama ba ta fahimtaba, da kuma marubci Ben Rhobes wanda ya kasance mai baiwa Barack Obama shawara akan harkokin waje bai gane ba shi ne, danagantakar Amurka da kungiyar PYD/PKK zai gurbata dangantakar Amurka da Turkiyya.

Babban abin lura anan shi ne, kamar yadda masana siyasa suke nazari, Turkiyya tana neman wa ta babbar kasar da za ta yi hurda da ita ba tare da ta kalubalanci tarihin daular Osmaniyya ta karnin 19 da kuma wadda ba za ta kawo cikas ga ‘yancin kasar Turkiyya ba.

Turkiyya ta zabi Amurka, a matsayar wannan kasar da zata iya hurda da ita bayan yakin duniya na biyu, sunyi hakan ne saboda rashin amincewa da kasar Rasha, ganin yadda suka jima suna gwagwarmaya da Rashan abinda yaki ci yaki cinyewa. Amurka ka iya kare Turkiyya daga dukkanin kalubalen Rasha musanman yadda Amurkan ta jibge sojojinta a Turkiyya lokacin Cold war. Yadda Rasha take kusa da Turkiyya ya sanya ganin cewa za ta kasance babban kalubale abinda ke damuwar dukkan dan kasar Turkiyyar.

Kasancewar duk da an kammala cold war kuma Rasha ta yi sanyi bai hanata zama kalubale ga Turkiyya ba. Shekaru 300 da suka gabata sun nuna cewar Rasha ta kasance babban kalubale ga Turkiyya, hakan ya sanya Amurkan kara samun damar ajiye ma’adananta a kasar Turkiyya domin ta kasance mai kula da rigingimun yankin.

2014 shekarar canji

Daga shekarar 2014, wannan lamarin ya canja, yadda kuma Turkiyyar ba ta ganin Rasha a matsayar wacce zata kalubalanceta. Musanman ma yadda Moscow ta kasance a Siriya yanzu, sabanin yunkurin gwamnatin Obama da yake hukuncin aiyanar da hurda da kungiyar PYD/PKK lamarin da yake kalubale ne ga Turkiyya. A takaice dai gwamnatin Obama ta zabi ta kalubalanci ‘yancin kasar Turkiyya.

Turkiyya na kalon dangantakar Amurka da kungiyar PYD/PKK amatsayin matakin da ka iya gurbata dangantakar kasashen biyu, saboda Amurka ta ba ta hurdarta da Ankara. Bayyana yadda Amurka ta tabka wannan kuskuren aiki ne na masana tarihi. Amma a yanzu zamu iya hasashen cewa gurguwar dabara, rashin hasashe da kyekyawar nazari ya sanya Amurka aikata wannan ragguwar dabarar.

Gulen ma kalubalene ga ‘yancin kasar Turkiyya

Abin bakin ciki, dangantakar Amurka da kungiyar ta’addar PKK bashi ne kawai matsalar dake tsakanin Ankara da Washington ba. Daga shekarar 2013 zuwa yau duk wanda yake nazari akan lamurkan kasar Turkiyya ya san cewa kungiyar asirin Fetullah Gulen kalubalece ga demokradiyyar Turkiyya. Yunkurin juyin mulkin da baiyi nasara ba a watan Yulin shekarar 2016 ya tabbatar da yadda kungiyar Gulen sukayi amfani da mambobinsu dake cikin sojojin kasar domin kifar da gwamnatin farar hula. Ya kamata kowa ya san cewa kungiyar Gulen ba ta kasance ba facce annoba ga al’umar Turkiyya da demokradiyyar kasar baki daya.

Kaman dai yadda kowa ya sani, Gulen ya kasance a Amurka tun shekarar 1999, hakan na nuni da baya ga hurdar da Amurka keyi da kungiyar ta’addar PKK/PYD tana kuma bada mafaka ga shugaban dake yunkurin tada zaune tsaye a Turkiyya da kalubalantar demokradiyyar kasar. Amurka tayi kememe akan bukatar mika Gulen ga Turkiyya duk da cikkakun hujjojin da aka bada dake nuna cewa su suka shirya yunkurin juyin mulki.

Akwai fa babban abin nazari anan, idan Washington ta kafa hurda da kungiyar ta’addar dake kalubalantar Turkiyya ta kuma baiwa wanda ke kalubalantar demokradiyyar kasar mafaka. Ashe sojojin Amurka a Turkiyya ba zasu kasance amatsayin kalubale a kasar ba? Ni dai ina ganin ba zasu kasance kalubale ba, amma ni ba dan kasar Turkiyya bane, ko dan siyasar Turkiyya dake da alhakin kare mutanensa daga dukkan kalubale. Ga ‘yan siyasan Turkiyya, masana siyasa da sojoji suna ganin lamurkan da suka faru a cikin shekaru biyar da suka gabata sun gurbata duk wa ta dangantaka dake tsakanin Washington da Ankara.

Indai zaka yi nazari mai inganci, zaka iya ganin cewa al’ummar Turkiyya na kallon sojojin Amurka a Turkiyya a matsayin kalubale ga ‘yancin kasar. Wannan na karantar da cewa yadda aka dauki Amurka amatsayan kasar amana a Turkiyya shekeru 70 da suka gabata lamarin ya canja. Idan mutun yayi wannan nazarin ya kuma gane yadda ‘yan kasar Turkiyya suka kai ga wannan hukuncin rashin amincewa da Amurka, zai gane ya kuma fahimci dalilan da suka sanya ‘yan kasar Turkiyya sukar Amurka dama kin amaincewa da ita a fannuka daban-daban.

Canji a matakan yau da kullun

Idan dai Amurka ta kasance kalubale ga ‘yancin Turkiyya ta yin hurda da kungiyar ta’addar PYD/PKK da kuma baiwa kungiyar asirin Fetullah Gulen gurin zama, tabbas ba za ta ci gaba da zama “offshore balancer” ba a idon Turkiyya, bi ma’ana wacce za a iya dogaro da ita da Turkiyya ta gano shekaru 75 da suka gabata. Sabanin haka za ta kasance tamkar kasashen da Turkiyya ke kallo a matsayar kalubale kamar yadda Ingila da Faransa suka kasance gareta a karni na 19 da kuma yadda Rash ta kasance a gareta shekaru 300 da suka gabata. Wadanda suka nemi ruguza daular Musuluncin Osmaniyya.

Idan gwamnatin Amurka ta taimakawa wa ta kungiyar dake neman rabe kasar Turkiyya, ta kuma baiwa wa ta kungiya da takasance kaulubale ga kasar Turkiyya. Ta sani cewa a idanun Turkiyya, ba ta da bambanci da kasashen Ingila da Faransa a karni na 19 ko kuma Rasha. A wannan yanayin shugabanin Turkiyya zasu nemi wa ta “offshore balancer”- aminniyar kasa ko kuma su dauki mataki da hannunsu.

Babban misali dai itace, yadda Turkiyya ta fara bayyana daukar matakan dogaro da kanta a fagen samar da makamai. A satin da ta gabata, Turkiyya ta bayyana samar da makamai da suka hada da matoci da jirage marasa matuka domin kalubalantar da kauda PYD/PKK daga Afrin.

Tun a karnin na 19, Daular Usmaniyya da Turkiyya sun kasance suna dogaro ga kasashen waje domin samun makamai dama horar da sojojin kasar. Amma a kwanakin nan a yayin yaki Fırat Kalkanı da ma na reshen zaitun da ake gudanarwa a yanzu gwamnatin Turkiyya tayi amfani da makaman zamani wadanda Ma’aikatar Kimiya da Fasahar Turkiyya ta kera.

Haka kuma, abin alfahari, a yayin hare-haren an dauki kwararan matakai da suka rage afkawa farar hula. Hakan na nuni da cewa sojan Turkiyya sun horu wajen iya yakar ta’addanci da ‘yan tada zaune tsaye, har da na birane dama Amurka ba ta iya kamalawa ba. Kuma bayan kammala yakin hukumomin bada agajin Turkiyya sun isa yankin domin taimakawa mazauna yankin. A takaice dai, Turkiyya na kauracewa dogaro ga makamai, kimiya da na’ururin kasashen waje.

Abinda da nike so in tabbatar anan shi ne, matakan da shugabanin Amurka suka dauka na da dana yanzu; su suka sanya shugabanin Turkiyya da sojojinta su dauki matakan da suka dauka. Idan Amurka tana son ta tabbatarwa al’ummar Turkiyya cewa ita kasace amintacciya lallai ya zama wajibi ta sake sabon salo da tsari.


 


Tag: YPG , PYD , PKK , FETO , Bakar Kasa , Amurka

Labarai masu alaka