Dalilan da suka gurbatar da dangantaka tsakanin Turkiyya da Amurka

A dai-dai lokacin da Turkiyya da wasu ƙungiyoyin adawa a Siriya suka cika wata ɗaya da gabatar da hare-haren reshen zaitun domin kauda ƴan ta'addar YPG daga Afrin. Dangantakar Turkiyya da Amurka ya ƙara tsami.

Dalilan da suka gurbatar da dangantaka tsakanin Turkiyya da Amurka

A dai-dai lokacin da Turkiyya da wasu ƙungiyoyin adawa a Siriya suka cika wata ɗaya da gabatar da hare-haren reshen zaitun domin kauda ƴan ta'addar YPG daga Afrin. Dangantakar Turkiyya da Amurka ya ƙara tsami, kasancewar Amurkan naci gaba da taimakawa ta'addanci. A yayinda Turkiyya dai ta kasance tana gudanar da wannan harin domin kare ƙasar Siriya da kuma kanta daga ƙalubalen ƴan ta'adda, Amurka kuwa na ƙoƙarin ci gaba da hurɗa da ƙungiyoyin ta'addancin ne. Haƙiƙa sanyin dangantakar ƙasashen biyu; waɗanda dukkan su mambobin NATO ne, baya ga lamarin baiwa ƴan ta'adda gudunmowa da Amurkan keyi, akwai waɗansu dalilan daban. Kasa aminta akan juyin juhanin ƙasashen Larabawa, goyon bayan juyin mulkin Misira da Amurkan ta yi da kuma tsayi bayan ƙungiyar FETO da suka yi yunkurin juyin mulki a ranar 15 ga watan Yulin 2016- sun sanya tangaɗin dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewar dangantakar Turkiyya da Amurka ya yi ƙamari a inda yake nanata cewar: ko dai a gyara ko kuma a ɓata baki ɗaya, hakan na nuni ga irin gurɓatar hurɗa ƙasashen.

Kasancewar Amurka ta kasa fahimtar halin da Turkiyya take ciki, kalaman Tillerson da yake cewa “ mun jima muna son mu tattauna da Turkiyya akan lamurkan yankin” na karantar da cewa Turkiyya ta ƙauracewa dogaro ga samun tsaro daga hannun Amurka. Haƙika kasancewar Amurkan ta kasa cika alƙawuran da ta yiwa Turkiyya, sun sanya Turkiyyar ɗaukar matakan da suka dace ƙwarara. A halin da ake ciki yanzu, zai ɗauki tsawon lokaci kafin Turkiyya ta sake amincewa da Amurka musamman akan fannin tsaro.

Daya daga cikin mataimakan firaministan Turkiyya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Bekir Bozdağ ya bayyana cewar, a yayinda Turkiyya ke daukar matakan kare yankunanta daga yunkurin ‘yan ta’adda ya zama wajibi ga Amurka da ta daina wasa da hankali da takewa Turkiyya akan lamurkan ‘yan ta’addar PKK/KCK/PYD/YPG, ya kuma kamata su sani, idan suka iya canja suna ko alama ba za su iya canja gaskiya ba kuma ba zasu iya yaudaran kowa ba, ya kuma kamata Amurkan ta amince da cewar PYD da YPG kungiyoyin ta’adda ne, ta kuma daina dukkan hurdar ta da kungiyoyin ta’addar da kuma dakatar da basu ilimi, makamai da ababen hawa. Bugu da kari, ta kuma karbe dukkanin makaman da ta rabawa kungiyoyin ta’addar yankin.

A cikin wannan halin ne ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya kawo ziyarta mai muhinmanci a Turkiyya. Baya ga dogon ganawar da yayi da shugaba Erdoğan ya kuma tattauna da takwaransa Çavuşoğlu. A tattaunawar, Turkiyya ta sake kira ga Amurkan akan abubuwan da ta nema a baya. Da farko dai, an aminta akan samar da wa ta tsari na musanmman a Mumbich dake arewacin Siriya, a yayinda Turkiyya ke ganawa da Amurkan ta bayyana aniyarta karara akan kauda kungiyar PKK/YPG.

Tabbas matsalolin dake faruwa tsakanin Turkiyya da Amurka bai ta’alaka akan lamarin PKK/YPG kawai ba.

A Amurka dai, ba’a amince da Turkiyya a matsayar kasar dake kokarin kare yankin ba, sai dai dora lamurkan kasar akan tunanin yunkurine na shugaba Erdoğan a kashin kansa da kuma kallon gwamnatin kasar mai tsatsaurar ra’ayi. A tsawon lokaci kafafen yada labarai sun kauda manofofin Turkiyya inda suka musanyasu akan hasashen wadansu abubuwa da suke yi. A dai-dai lokacin da Amurka ke neman a kare hakkin bil- adama a Turkiyya, ta kauda fuskanta akan lamurkan kare hakkin dan adam a Haddadiyar Daular Larabawa, Saudiyya da Misira dake  gabas ta tsakiya. Wannan tabi’ar na Amurka bai kasance ba facce don ta sanya ido akan yadda Turkiyya ke gudanar da hurdarta da sauran kasashen waje.

Bugu da kari, a yayinda ake yunkurin juyin mülkin 15 ga watan Yuli, sanarwar da Amurka ta fitar da cewa ta na nazarin ko akwai yunkurin juyin mülkin, da kuma matakan da ta dauka na amanna da wadanda su kayi yunkurin juyin mülkin, duk da ta goyi bayan al’ummar kasar Turkiyya, sun kasance manyan abun da suka juya ludayin dangantakar kasashen biyu. Haka kuma kasancewar ‘ya ‘yan kungiyar FETO a Amurka da kuma samun goyon bayan daga hukumar leken asirin CIA ya kara gurbatar da hurdar Amurka da Turkiyya. Duk da kwararan dalilan da Turkiyya ta baiwa Amurkan akan cewar shugabanin kungiyar FETO dake Amurka su su ka gudanar da yunkurin juyin mülki, Amurkan taki ta mika su ga Turkiyya kamar yadda ta bukata.

Daya daga cikin manyan lamurkan da su ka gurbatar da dangantakar dake tsakanin Turkiyya da Amurka shi ne juyin mülkin daya kifar da gwamnatin Muhammed Mursi a Misira. A yayinda Turkiyya ke kokarin kare zabbeben shugaban Misira na farko bayan juyin juhani, Amurka na kallon Turkiyya amatsayar wacce ke daukar matakan kare gwamnatin Islama, haka kuma, a yayinda Amurkan ke murna da juyin mülkin da Sisi ya aiyanar, Turkiyya naci gaba da baiwa hukumar Mursi gudunmowa- hakan na nuni ga raba hannun rigar Turkiyya da Amurka a gabas ta tsakiya. A dai-dai lokacin da Turkiyya ke bukatar samar da hukumomin da al’ummar kasashen gabas ta tsakiya su ka zaba da kansu; Amurka na yunkurin kafa shugabanin da za su zama ‘yan kwaironta da kuma kare manofofinta ko ba dadi. A bisa ga ra’ayoyin da su ka yadu a Amurka dai, shugabanin da za su hau mülki bisa ga zabe mai inganci; ba za su kare ra’ayoyin Amurka ba, sai dai ma su kalubalance su.Labarai masu alaka