Hare-haren da Turkiyya ke kaiwa 'yan ta'adda a Siriya ya fara haifar da da mai ido

A yanzu haka ana ganin irin ci gaban da aka samu a kasar Siriya, musanman yadda Turkiyya ke gaf da kammala hare-haren reshen zaitin da ta kaddamar a kasar domin kauda ‘yan ta’adda a sati biyun da suka gabata.

Hare-haren da Turkiyya ke kaiwa 'yan ta'adda a Siriya ya fara haifar da da mai ido

A yanzu haka ana ganin irin ci gaban da aka samu a kasar Siriya, musanman yadda Turkiyya ke gaf da kammala hare-haren reshen zaitin da ta kaddamar a kasar domin kauda ‘yan ta’adda a sati biyun da suka gabata. Hakika rundunan sojar Turkiyya ta samu nasarori ma su dama akan samar da lumana a yankin Idlib. Wannan ci gaban da aka samu dai ya taba damar da Amurka ta ke dashi a Siriyar.

Ko shakka babu wannan hare-haren reshen zaitin da Turkiyya ta kadamar, baya ga kauda ‘yan ta’addar PKK/YPG a kasar Siriya zai kuma rage mu su kwarin gwiwa da karfi a wadansu yankunan da su ke. Da hakan ne su ka fara gwadawa al’ummar Menbich, Haseke, Rakka da Deyr Az-zor azaba, lamarin da ya sanya al’ummar Menbich kalubalantarsu. Kasancewar yadda Amurka ke daukar matakan da ba su dace ba a yankin, ya sanya manyan kasashen yankin kaurace ma ta; inda su ka barta tilo, su ka gudanar da taron samar da lumana a Siriya da haddin gwiwar kasashen Rasha, Iran da Turkiyya a Astana. Haka kuma ganin yadda rundunar sojan Turkiyya ta kebe tsaunukan Al-Eys  da ke Idlib ya tabbatar da irin kwarin gwiwar da kasar Turkiyya ke dashi a Siriyar.

Duk da irin kalubalen da ba’a rasa ba, rundunar sojan Turkiyya da haddin gwiwar ‘yan adawar Siriya, sun sami nasara sosai. Tsaunukan da su ka karbe daga hanun ‘yan ta’adda na nuni ga irin nasarar da aka samu. Wannan matakin da Turkiyya ta dauka ya kauda tunanin da akeyi da cewar kungiyar ta’addar YPG ta gagara inda ta kuma wai ta zama kaka gida a yankin. Wannan gagara badau din da ake ganin kungiyar YPG ta yi nada asaba ne da gudunmowar makaman da Amurka ke ba ta. Kamar yadda aka sani, mafi yawan mazauna yankin da kungiyar ‘yan ta’addar YPG su ka yi kakagida, Larabawa da Turkmen ne da kungiyar YPG ke takurawa. Kasancewar ta’asar da kungiyar YPG ta ci gaba da aikatawa duk da an kauda kungiyar DAESH, ya sanya al’ummar yankunan sanya alamar tambya akan kungiyar. Da hakan ne larabawan kasar Turkiyya, Kurdawa daga cikin ‘yan adawa da Turkmen sun ka dauki matakin samar da wa ta mafita ta kalubalantar kungiyar YPGin a yankin. Musanaman a yankunan Menbich inda kungiyar YPG ke kaddamar da zalunci iri daban daban ga al’ummar kasar. Hare-haren reshen zaitin da aka fara dai ya kara karfafa Larabawa, Turkmen da Kurdawan yankin akan kalubalantar zaluncin da kungiyar ta’addar YPG ke gudanarwa a yankin.

A gaskiyar lamari, wannan hare-haren reshen zaitin ba’a kaddamar da shi don kauda kungiyar YPG kawai ba, har da kauda dukkan irin gina ta da Amurka ta yi a kasar Siriyar. Ganin yadda Amurka ta fitar da sanarwa daban-daban akan Turkiyya da kuma yakin da ake gudanarwa a Afrin, ya tabbatar da cewa Amurkan na fama da rudani a cikin gidan ta. Haka kuma, ma’aikatun Amurkan na sabawa junansu musanman yadda a ‘yan kwanakin nan aka ga kungiyar YPG da kasar ke hurda da ita a cikin jerin kungiyoyin ta’addancin da hukumar leken asirin CIA ta lissafa.

A yayinda Rasha, Turkiyya da Iran su ka gudanar da taron Astana domin samar da lumana a kasar Siriya, Amurka ta kasance ‘yar aware a yankin, musanman a dalilin aiyanar da gurguwar dabararta na amfani da wa ta kungiyar ta’addanci domim kauda wa ta. Kasashen Rasha, Turkiyya da Iran dai sun kalubalanci yunkurin PYG dake kalubalantar samar da zaman lafiya a Siriya da kuma shirin Amurka na kafa wa ta rundunar soja a yankin. Ko shakka babu anyi nasarar rage kaifin dangantakar Amurka da YPG, lamarin da ya sanya Amurkan sake sabowar salon aniyar kafa wa ta rundunar ‘yan ta’adda a yankunan.

Daya daga cikin muhimman ci gaba da aka samu a Siriya, itace kafa yankunan sa ido da rundunar sojan Turkiyya su ka yi a Idlib. Haka kuma sunyi nasarar samar da kwanciyar hankali da lura da yankin AL-Eys.

A ’yan kwanakin da su ka gabata; Turkiyya ta kasance a sahun gaba a idanun duniya da ke kokarin kauda take hakkin dan adam, da kisar kiyashi a Siriya, musanman idan aka yi la’akari da rawar da ta taka a yarjejeniyar Astana.

Kasancewar Turkiyya a matsayar ja gaba a lamurkan Siriya nada alaka da gudunmowar da take baiwa Siriyawan. Yanzu haka akwai Siriyawa fiye da miliyan uku a kasar Turkiyya da kasar ke daukar nauyinsu yau da kullun, haka kuma kasar Turkiyya na aika gudunmowa ga Siriyawa fiye da miliyan hudu a Siriyar ta fannunka daban-daban.

 Labarai masu alaka