Take Hakkokin Dan Adam da Kungiyar Ta'adda ta PYD/YPG Ke Yi

Tun bayan kafa kungiyoyin PKK/KCK zuwa yau, su ke cutar da takurawa mazauna gabashi da kudu maso gabashin yankin Anadolu ta hanyar kai hare-haren ta’addanci a kauyuka, kisa, tsoratarwa da tilastawa al’ummar yankin kaura.

Take Hakkokin Dan Adam da Kungiyar Ta'adda ta PYD/YPG Ke Yi

Tun bayan kafa kungiyoyin PKK/KCK zuwa yau, su ke cutar da takurawa mazauna gabashi da kudu maso gabashin yankin Anadolu ta hanyar kai hare-haren ta’addanci a kauyuka, kisa, tsoratarwa da tilastawa al’ummar yankin kaura. Da hakan ne su ke nuna gagaransu ga al’ummar yankin. Ire-iren wadannan cin zalin ne barayin kungiyar a Siriya watau PYD/YPG ke gudanarwa akan al’umar kasar.

A aniyarta nayin kaka gida a yankin ne take gudanar da laifukan take hakkin dan adam ga kabilun Kurdawa, Larabawa, Turkmen da Azidi. Wadannan laifukan take hakkin dan adam da take gudanarwar, duk da kungiyar kare hakkin bil’adama ta lura da hakan inda ta fitar da wata sakamako akan lamarin. A dalilin cin zarafin da kungiyar PYD/YPG ke aiyanarwa a yankin da yawan mazauna yankin sun ficce inda su ka koma ‘yan kudun hijira a wasu yankunan. Da yawansu sun zabi shigowa Turkiyya wacce ta bude kofarta a garesu. Duk da ire-iren wadannnan cin zalin da cin zarafin da kungiyar PYD/YPG ke aiyanarwa ga farar hula wasu manyan kasashen duniya sun zabi hadaka da su da sunan yakar kungiyar ta’addar DEASH. A maimakon yakar DEASH sun dinga amfani da gudunmowar makaman da suke samu wajen kalubalantar mazauna yankin da su ka hada da Kurdawa, Larabawa da Turkmen.

Misali, idan muka dubi sakamakon binciken Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Siriya (SNHR) a watan Janairun shekarar 2016. Zamu ga yadda ta fede biri har wutsiya akan yadda kungiyar PYD/YPG ke kisar gilar kabilun yankin, tilasta musu shiga ta’addanci da kuma yin hijira daga yankin. A sakamakon binciken sun bayyana cewar 16 daga cikin mata 43 da yara 51 da suke shan azaba karkashin kungiyar suka rasa rayukansu. A jumlace kungiyar ta halakar da farar hula 407.

Haka kuma, wa ta bincike da kungiyar saka ido akan hakkin dan adam (HRW) ta yada a shekarar 2014 mai taken “Under Kurdish Rule: Abuses in PYD-Run Enclaves of Syria” ta bayyana cewar kungiyar PYD/YPG ta dinga azabtar da wadanda take ganin ‘yan adawarta ne a yankin, ta hanyar kame su da daure su da kuma gana musu azaba. Musanman ma Kungiyar Demokradiyar Kurdawa (PDKS), dake kalubalantar lamurkan PYD din mambobinta sun ga ta’asa a hannun ‘yan kungiyar PYD.

Bari mu dan bayyana daga cikin kisar gillar kabilun da kungiyar PYD/YPG ke aiyanarwa. Daga cikinsu dai akwai:

TSARE DA CIN ZALIN ‘YAN ADAWARSU

Kungiyar PYD/YPG da ta rasa wa ta mafita ta fara kaddamar da tsare kungiyoyin dake adawa da aiyukan ta’addancin da ta ke aiyanarwa. Ta’asar kungiyar dai ya soma ne a watan Oktobar shekarar 2011 a lokacin da ta fara da kashe shugaban Jam’iyyar ci gaban Kuradawa Misel Temolamarin da ya sanya Kurdawan kara kalubalantar dukkan aiyukan kungiyar PYD.

PYD/YPG sun ci gaba da irin wannan kisar gillar inda suka kashe shugaban masu tsatsaurar ra’ayi Abdullah Bedro da wakilin jam’iyyar Haddin Kan Kurdawa a Halep Serzad Haj Rashid.

Bugu da kari, shi kanshi shugaban Demokradiyar Kurdawa a Siriya Salah Bedreddin sai da ya yi hijira ta Jamus zu wa Erbil domin kubucewa fitinun kungiyar ta’addar.

Kafin soma yakin Siriya akwai kungiyoyin Kurdawa 12 a kasar amma a yanzu PKK/PYD kawai suka rage; a yayinda dukkan sauran sun tsere daga yankunan da PKK/PYD din ke kama karya. Kusan Kuradawa dubu 350 su ka nemi mafaka a Turkiyya kuma har ila yau suna rayuwansu a kasar.

A ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2013 al’ummar garin Amude sun fito inda suka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da aiyukan PYD/YPG. A yayin wannan zanga-zangar mambobin kungiyoyin PYD/YPG su ka bude masu wuta lamarin da ya yi sanadiyyar rayuka 8. A cikin wannan lokacin ne wasu mabobin kungiar PYD/YPG su ka kame shugabanin wa ta jam’iyya 50 inda su ka tusa kyeyar su zuwa ofishin nasu sunka kuma yi musu na kare.

UQUBA DA ZALUNCIN DA WADANDA SUN KA KAMA KE FUSKANTA

Kungiyar kare hakkin dan adam ta fitar da wa ta sanarwa inda ta bayyana yadda rudunan ‘yan sandar kugiyar ta’addaci mai suna “Asayish” ke kama karya da cin zarafin alummar yankin da take tsare da su. A cewar kungiyar kare hakkin dan dam ( HRW) a lokacin da kungiyar ke tsare da Hannah Hamdoş, a Afrin ya rasa ransa sanadiyar buga kanshi da wani dan kungiyar PYD/YPG ya yi ga bango, haka kuma a watan Febrilun shekarar 2014 wani mambar kungiyar “Asayiş” ya kashe wani dan shekara 24 Raşwan Ataş a Sere Kaniye.

Ganin dai yadda daga shekarar 2012-2014 aka samu lamurkan kisa da batan mutane tara da ba’a gano ba wadanda kuma dukkansu mambobin kungiyoyin dake adawa da PYD/YPG ne ya sanya alamomin tambaya da dama a yankin.

AZABTAR DA MATA DA YARA

Kungiyar PYD/YPG da ke neman kara ikonta a Siriya da kuma kare karfinta; ta dinga gwadawa wadanda ke adawa da ita azaba daga cikinsu har da mata da yara ba ta bari ba.

Wannan ta’asar PYD/YPG kungiyar kare hakkin dan adam ta bayyana shi ne a watan Janairun shekarar 2016, inda ta tabbatar da cewar a tsakinin shekarun 2011-2016 kungiyar ta kashe mata 42. Daga cikin matan akwai wa ta da ke zaune a kauyen Say Ghoul din Halep mai suna Nabiya El Salah wacce ‘yan kungiyar su ka kasheta a hanyar ta ta zuwa Rakka –Tel Abyad da harbi uku a ranar 14 ga watan Agustan 2015.

A sakamakon binciken kungiyar kare hakkin dan adam din kuma, kungiyar ta kashe wata mata mai suna Tarfa Halil el Hasud mai shekaru 58 a gidanta bayan sun kashe mijinta a baya. Haka kuma kungiyar ta’addar PYD/YPG a tsakanin watan Janairun 2014 zuwa Oktobar 2015 sun tsare mata 88 da sunan tilasta su shiga sojan döle a garuruwan Haseke, Kamishli da Afrin.

KISAN KIYASHI DA TIRSASA WA JAMA’A YIN HIJIRA

A yankunan da kungiyar da ta’adda ta PYD/YPG ta fi tasiri, akwai kabilun Larabawa,Turkmen,Suriniyawa,Armeniyawa da dai sauran su, bila adadin. Haramtacciyar kungiyar wacce ke kokarin tankwara dukannin lardunan da ta mamaye a karkashin inuwar mulkinta, na ci gaba da tirsasa wa mutane yin hijira ta hanyar rugurguje matsugunansu da nufin takaita yawan al’uma.

A cewar rahoton kungiyar kare hakkin bil adama na kasar Siriya (SNHR), kimanin iyalai 100 na kabilun Turkmen da ke Haseke sun fuskanci wulakanci da tirsasawa.An raiwato cewa,a tashin farko an tilasta musu yin kaura zuwa wasu yankuna,inda daga bisani kuma matsanancin halin rayuwa yasa suka nemi mafaka a Turkiyya.

A rohoton da SNHR da ta fitar a watan Oktaban shekarar 2016,kungiyar ta'adda ta PYD/YPG ta kusa kai a yankunan da babu wani Bakurde ko daya,inda ta dinka kisa gilla,rushe muhallai da kuma tilasta wa mutane yin hijira. A cewar rohoton, PYG/YPG ta tirsasa wa dubban mutane wadanda yawancin su Larabawa ne yin hijira da kuma rugurguje muhallansu.Duba da ayar doka ta 8 ta yarjejeniyar Roma, dukannin wadannan ababen da haramtacciyar ta aikata, dadai suke da laifuffukan yaki, cin zarafi da kuma take hakkokin bil'adama.Haka zalika,an tabbatar da cewa an yi raga-raga da garuruwa 9 har illa mashallah tare da tirsasa wa al'umominsu yin hijira, a yayin da suka yi gunduwa-gunduwa da kauyuka 19 tare da korar dukannin mutanen da suke kyama.Baya ga haka,a illahirin kauyukan da ta mamaye,PYD/YPG ta kore wadanda ba Kurdawa ba daga yankunansu ta hanyar yi musu barazana da kuma tayar musu da hankali.A jimillance akalla dubban mutane ne aka tirsasa wa yin hijira daga yankuna 49.

An sanar da cewa a ranar 26 ga watan Mayun shekarar 2016, kungiyar ta'adda ta PYD/YPG ta bai wa al'umomin sama da kauyuka 26 na kudancin garin Haseke da ke kasar Siriya awanni 24 don su gaggauta ficewa daga matsugunansu. A cewar shaidar daya daga cikin mazaunan yankunan da lamarin ya shafa, zuwan PYG/YPG ke da wuya aka dinka gasa aya a hannayen kabilun Larabawa babu dare babu rana.Saboda 'yan ta'addar sun bayyana cewa,Labarawa da Turkmen basu da gurbi a yankin Kurdistan.A daya gefen kuma,an rawaito cewa a watan Fabrairun shekarar 2015,an tsare akalla iyalan Turkmen 100 inda aka dinka azabtar da su babu gaira babu dalili. Abinda yasa suka guje daga gidajensu,inda suka nemi mafaka a kasar Turkiyya.A wani rahoto mai taken "Babu inda zamu" da kungiyar kare hakin bil'adama ta Amnesty International ta fitar,wanda ke kunshe da bayannan shaidun gani da ido,an gabatar wa duniya laifukan kisan kiyashi, tirsasa jama yin hijira da na ruguje-rugujen da PYD/YPG ta aikata.

A cikin rahoton akwai sakamakon bincike da kuma hirarrakin da aka gudanar da mutanen da suka yi saura a kauyen Larabawa na Hüseyiye dake a yankunan karkara na Tel Hamis,bayan ruguje-rugujen da haramtacciyar kungiyar ta yi.A sa'ilin da aka kwantata hotunan da tauraron dan adam ya dauka tsakanin watan Yunin 2014 da 2015,an gano cewa a cikin shekara 1, PYD/YPG ta rushe kashi 94 a cikin dari na binaye 225 da kauyen ya kunsa,inda a yanzu haka gine-gine 14 kacal suka yi saura.

Daya daga cikin masanan Amnesty International,Lema Fakih ya ce :"PYG/YPG ta rushe muhallai da tirsasa wa dubban daruruwan fararen hula yin hijira daga yankunansu.Kungiyar ta'addar ta yi wa doka da oda zagon kasa,inda ta yi watsi da dokokin kasa da kasa.Abinda ke nuna cewa ta yi aikata laifukan yaki da gangan.

YARA KANANA MAYAKA

Kungiyar ta’adda ta PYD/PKK na ci gaba da sanya yara kanana a cikin yaki yankunan da ta kwace a kasar Siriya domin samun damar ci gaba da shugabantar yankunan.

Akwai yarjeniyoyi da dama na kasa da kasa da suka hada da ( Dokar 1949 da ta nemi a kare fararen hula a lokutan yaki, da kuma yarjejeniyar kare hakkokin kanan yara ta Majalisar Dinkin Duniya) amma duk da haka ‘yan ta’addar PYD/PKK suna ci gaba da saka yara kanana a harkokin yaki inda suke karya wadannan dokoki

Kwamitin Musamman na Majalisar Dinkin Duniya mai bincike kan Siriya a ranar 16 ga watan Agustan 2013 ya fitar da rahoton cewa, a Afrin da Haseke ‘yan ta’addar PYD/PKK sun saka wsu yara mace da namiji masu shekaru 12 a harkokin yaki.

A rahoton Majalisar Dinkin Duniya game da sanya yara kanana yaki a Siriya an bayyana cewa, a yankin Haseke akwai yara masu shekaru tsakanin 14-17 wadanda suke mambobin kungiyar ta’addar ne kuma suna shiga yaki a fafata da su.

A rahoton cinikin dan adam da Amurka ta fitar a watan Yunin 2016; an bayyana cewa, kungiyar ta’adda ta PYD/YPG na ci gaba da dauka, horar wa tare da sanya yara kanana da ba su wuce shekaru 15 ba da suka hada da maza da mata yaki. Rahoton ya kuma kara da cewa, a watan Afrilun 2015 ‘yan ta’addar PYD/YPG sun yi garkuwa da wata yarinya mai shekaru 15 a Afrin duk da korafin da iyayenta suka bayar.

Kungiyar sanya idanu kan hakkokin dan adam ta fitar da wani rahoto a shekarar 2014 mai taken “A karkashin Gwamnatin Kurdawa”. Rahoton ya zargi ‘yan ta’addar PYD/YPG/YPJ da saka yara ‘yan kasa da shekaru 18 yaki. Kungiyar ta nuna jerin sunayen yara kanana 59 wadanda 10 daga cikinsu na da shekaru kasa da 15.Labarai masu alaka