Illolin Manyan Kasashen Duniya ga Kasashenmu

Matsalolin Yankunanmu: Shin yaya ne rikice-rikicen yankunanmu ba zasu warwaru ba, tare da tallafin masu fada a ji na kasa da kasa?

Illolin Manyan Kasashen Duniya ga Kasashenmu

Matsalolin Kasashen Duniya -05

Zamu yi nazari kan sharhin Farfesa Kudret Bülbül,Shugaban Tsangayar Nazarin kimiyyar siyasa Ta Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara.

A 'yan shekarun nan, babu wata kasar da ta samu kwanciyar hankali,sakamakon tallafin masu fada a ji na duniya ko kuma na kawacen sojojin da suke jagoranta. Hasalima,ana iya cewa masatloli na ci gaba da wanzuwa a dukannin  kasashen da suka yi kacibus da taimakonsu.Da yawa daga cikin wadannan kasashen sun kara zubar da kwalla, fama da matsanantan matsalolin hijirce-hijirce,asarar rayuwa da karyar tattalin arziki,tare da   zama tamkar jahananma ga al'umominsa.A gaggauce zamu duba irin rawar da masu fada a aji na duniya suka taka a wasu rikice-rikicen da suka kunno kai a baya bayan nan,da zummar kara bankado wannan gaskiyar. Tarayyar Soviyet ta kusa kai a tarihi.Amma, duk da halin ha'ula'i da al'umarta ke fuskanta,kawo yanzu Afganistan ta kasance a cikin ukuba,sakamakon rikicin da ya kunno kai,tun a lokacin da Rashawa suka yi yunkurin mamaye ta.Babu makawa,Saddam Hussein shugaba mai mulki kama karya.A karakashin mulkinsa,an sha fama da matsaloli masu yawan gaske.Amma idan muka yi la'akari da yadda kasar Iraki ta koma a yau,zamu iya dasa ayar tambaya cewa, shin kashi nawa na 'yan kasar Iraki ne zasu fifita halin suke ciki a yau kan rayuwar da suke da ita a zamanin Saddam Husain ? Shin wane tabbaci ne 'yan kasar Libiya wacce aka yi wa gunduwa-gunduwa tare da yin wasoso da dukiyoyi da kuma albarkatunta,ke da shi game da yadda kasarsu zata kasance a gobe ? Sham fa ?Shin,a kasar da an tirsasa wa kusan illahirin al'umarta yin hijira tare da kashe dubban daruruwa daga cikin su,a kasar da ta kasance cibiyar wayewa,a Siriya wacce daya daga cikin biranenta Aleppo ya zama wuri mai wuyar rayuwa,waye ne zai iya hasashen wata makoma tare da tallafin masu fada a ji na kasa da kasa.

A yau Amurka na yi wa kasar Pakistan, wacce ta biya diyyar yakin da aka kwashe shekaru 10 ana yi a Afganistan, barazana.Abinda yasa take fama da babbar matsala,idan aka kwatanta da shekarun baya.

Masu fada a ji na kasa da kasa, ba su nuna damuwa ba game da matsalar Musulman Arakan wadanda gwamnatin Myanmar ta  kone gidajensu kurmus tare da yi musu kisan kiyashi da kuma tirsasa su yin hijira zuwa Bangaladesh,sabili da mabiya addinin Islamar ba zasu iya neman mafaka a Yammacin duniya ba, don ta yi musu nisa.Haka zalika babu tabbacin zasu nuna adalci a wannan lamarin a sa'ilin da hankalinsu ya dawo kan ukubar Rohingya.Sanin kowa ne, ya ababe suka kasance a Falasdinu a karshen wannan karnin, bayan rawar da masu fada a ji na kasa da kasa suka taka.A duk safiyar Allah fadin Falasdinu na ci gaba da ragewa,sakamakon yadda Isar'ila ke mamayar yankunanta da kuma take 'yancin 'yan kasarta.Abinda yasa Falasdinawa ke a rayuwa a cikin wani yanai wanda yayi kama da na gidan wakafin da rabinsa ke bude.Ko shakka babu,misalai na iya daduwa.A gaskiya abin bakin ciki ne,amma dukannin rikice-rikicen da muka gabatar a sama,matsaloli ne da kasashen duniyar Islama ke fama da su.Wannan lamari  ne da ya kamata a  bayar da cikakken bayani da kuma zurfafa bincike a kansa.

Me ya sa matsalolin suke kara ruruwa saboda tsoma bakinmanyan kasashen duniya?

Shin ko me yasa matsaloli ke ci gaba wanzuwa a duk lokacin masu fada a ji na duniya suka kawo tallafi ? Watakil dalili na farko shi ne tunanin da suke masu fada ajin ke da shi.Dokokin kasa da kasa ba su da alaka da adalci,hakkin bil adama, ko kuma darajar mutunci.Abar da suka fi bai wa karfi ita ce ribar da zasu samu.Bayanin da ,wakiliyar kasar Amurka a Turkiyya,misiz Kati Piri  ta yi a cikin rahotonta na wannan makon, inda ta bayyana cewa kisan gillar da kungiyar ta'adda ta PKK ta yi  wa mutane dubu 40, ba wata barazana ce a gare su ba, na kara nuna irin manufar da suka gaba.

Wannan ra'ayin na yin nuni da cewa, idan har ba hari aka kai musu ba, to hankalinsu ba zai taba tashi ba,kana ba zasu taba nuna tausayi, ko kuma daukar wani mataki daya tilo, daidai daya rana, da zummar kawo wa duniya dauki.Wannan tunanin yayi hannun riga da wayewar duniyarmu.Domin bama kallon kowace matsala da idanun masu mulkin mallaka.Ba zamu taba kwaikwayi wadanda ke iya take duk wata ka'ida,da nufin cimma burin da suka gaba ko ta halin kaka,ta hanyar shirya makarkashiya da manakis.A duniyarmu,yaki ma na da nasa ka'idoji.Ba wai yin amfani da doka da oda a matsayin makamin yaki ba,a'a ina nufin zayyana ka'idojin yaki duba da doka da oda.Saboda a cikin wannan yanayin ne,muke yi wa yaki kwallon halatacce.

Ko shakka babu wadannan masu fada aji na kasa da kasa, na yunkurin warware matsalolin da suka kuno a yankunanmu ma, duba da manufofi da kuma bukatunsu kamar yadda muka bayyana a baya.Abinda yasa muna iya cewa, akwai yiwuwar su ne umma'aba'isar tashe-tashen hankulan da ke afkuwa a yankunanmu, ko kuma muce su ne ke hura wutar duk wata fitinar da ke kuno a duniyarmu,musamman a duk lokacin da suka bukaci cuta wa junan su.Suna iya amfani da kasashen yankunanmu don cuta wa kasashen duba da manufofinsu.A wani sa'ailin ko da ko basu haddasa matsalolin yankunanmu ba,suna bukatar ganin mu dawwama a cikinsu.Shi yasa a kulli yaumin suke fitar da sabbin tsare-tsaren don cimma burinsu.Kuma kaka gidar Amurka ta yi a Sham,wani babban misali ne.Haka zalika, rikice-rikicen yankunmu sun zama wata damar tara dukiya ga kasashen yamma,inda a yanzu haka suke ci gaba da siyar da makamai masu dumbin yawa.

A gefe daya kuma, basu faye nuna damuwa da irin halin ni 'yasu da al'umomin yankunanmu suka tsinci kansu a ciki sabili da tsahe-tashen hankula.Shi yasa kasashenmu ne biyan diyya mafi girma.Haka zalika ba a kullin yaumin ba ne a gani masu fada a ji a yankunanmu.Don haka ne fitintinun da ke bullowa a yankunanmu, bayan tsirran fitinar da suka shuka, basa shafar su.Idan ana son a warware matsalolin da muka bayyana a baya, dole ne a kasashenmu su hada kai.Domin kasashen waje babu wata sarar da zasu yi.Ko shakka babu, ba masu fada a ji kawai ne ke da hannu dumu-dumu a wajen bullowar matsaloli a yankinmu.Duk da yake a yawancin lokuta, tare da tallafinsu ne wutar rikice-rikice ke dada ruruwa.A daya bangare kuma, kura-kuren da kasashen yankinmu suka tafka,wani mau'du'i ne daban.Idan har ba a nemi maganin matsalolinmu a yankinmu ba, do masu fada aji na duniya ba zasu taba shafa mana lafiya ba.

Akwai yiwuwar mu fara duba manufofin da ke da alaka da mazhaba,kabilanci da na mulkin mallakar  da wasu  kasashe makwabtanmu ke yadawa.Domin kasashen waje na bugun gaba da wadannan ababen da ci gaba da kusa kai a yankunanmu. Amma kamar yadda muka bayyana a baya, mamaikon su warware matsalolin kasashenmu,masu fada a ji na duniya na kara rura wutar fitina.Abinda yasa a kullum, matsaloli ke ci gaba da samun gindin zama da fafaduwa.Shi yasa al'umomin da suka sher shekaru dubu suna rayuwa tare, a yau suke ci gaba da kashe junan su,wanda hakan ke kara rage martabar yankinmu.Shi yasa, duk yadda ta kasance, kamata yayi a bai wa kasashen yankinmu damar warwarwe matsalolinsu da kansa ba tare da an gayyaci wani bare ba.  

Matsalolin Kasashen Duniya -05

Matsalolin Yankunanmu: Shin yaya ne rikice-rikicen yankunanmu ba zasu warwaru ba, tare da tallafin masu fada a ji na kasa da kasa?

Mun gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bülbül, shugaban tsangayar kimiyyar siyasa ta jami’ar Yıldrım Beyazıt da ke birnin Ankaran kasar Turkiyya.Labarai masu alaka