Siyasar Tattalin Arziki

Bisa ga nasarorin da aka samu a fannoni da dama, ya kamata mu yi sharhi akan bunƙasar tattalin arzikin duniya dama na Turkiyya acikin shekarar 2017, tare da tunatar wa akan habbakar tattalin arzikin kasar duk da ƙalubalolin da ta fuskanta.

Siyasar Tattalin Arziki

Ya kamata mu dubi irin matakai da Turkiyya ta dauka bayan yunkurin juyin mulki a shekarar 2016 da kuma nasarar da tattalin arzikin ƙasar ya samu a cikin shekarar 2017. Daga cikin ababen da zuma yi nazari akan su, sun haɗa da haɓɓakar kayayyakin da ake fitarwa, alƙaluman dake nuni ga bunƙasar tattalin arziki da kuma ƙaruwar aikin yi a ƙasar. Wadannan nasarorin sun isa su zamo hujja ga irin bunƙasar da tattalin arzikin Turkiyyar ke ciki.

Acikin kwata na uku a shekarar 2017, tattalin arzikin Turkiyya ya samu bunƙasa da alƙaluma 11.1, da hakan ne ƙasar ta kasance wacce tafi ko wacce bunƙasa daga cikin ƙasashen G-20 da OECD. Tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da ƙaruwar kaso 7.4 acikin watanni taran farkon shekarar 2017, lamarin da ya ci gaba har karshen shekarar.

 Ana hasashen tattalin arzikin acikin 2018-2020 zai samu ƙaruwar kaso 5.5, hakan na da alaƙa da mataki matsakaicin zangon da kasar ta dauka, buga da ƙari, hasashen ya nuna tattalin arzikin zai ƙaru acikin shekarar 2018 da kaso 6.5 zuwa 7.5 cikin ɗari fiye da yadda ya karu a cikin shekarar 2017.

Ɗaya daga cikin bangarorin da ke nuni ga bunƙasar tattalin arzikin shi ne ƙaruwar aikin yi, a cikin shekarar 2017 anyi nasarar samun ƙaruwar aikin yi a ƙasar, musamman a watan Satumba da aka samar da aikin yi har milyan ɗaya da dubu 233, hakan dai na nuni da ƙaruwar kaso 11 cikin ɗari.

Hakan dai ya samu ne a dalilin matakan da gwamnatin kasar ta dauka a cikin shekarar da aka baiwa ma'aikatu tallafi da kwarin gwiwa, lamurkan da ya habbaka aiyukan su har ya ba su damar ɗaukar aiki. Wannan matakin dai ya sama wa fiye da mutum miliyan ɗaya aiki a yau.

Tabbas, duk da wannan ƙaruwar aikin yi, bai sanya rashin aikin yi raguwa zuwa darajar da ya kamata ba. Babban dalilin hakan shi ne ƙaruwar masu niyya da neman aikin yi a cikin ƙasar, sabili da haka ruguwar rashin aikin yi lamari ne da ka iya daukar ƴan lokuta.

A sashen fitar da kayayyaki kuwa, injunan mota ne suka samu tagomashi, a yayinda akayi nasarar sayar da injuna har na biliyan 142 a shekarar 2016, haka kuma a dalilin matakan bunƙasar da fannin da aka yi ana hasashen fitar da injuna har na biliyan 158 a shekarar 2018.

Ɗaya daga cikin lamurkan da suka taɓa tattalin arzikin Turkiyya a 2017 shi ne tashin farashin kayayyaki da  ƙaruwar kaso 12.98 cikin ɗari, sai dai wannan lamari ne da ya shafi kusan duniya baki ɗaya musamman idan muka dubi lamarin kasuwar canji a shekarar 2017.

 A ɗayan barayin kuma, an samu ƙaruwa kuɗaɗen shiga idan aka kwatanta kasafin kudin shekarar bara da na 2017. Haka kuma anyi nasarar rufe gurbin naƙasun kasafin kudin da aka samu da kaso uku cikin ɗari, har ila yau da ƙaruwar asusun bashin jama'a da kaso 28.5 cikin ɗari bisa ga ma'aunin Maastricht akan kaso 60 cikin ɗari zamu iya cewa a wannan fanni an samu nasara sosai.

Daga karshe dai za mu iya  hasashen cewa tamkar yadda tattalin arzikin Turkiyya ya habbaka a cikin shekarar 2017 zai ci gaba da bunƙasa ma a cikin shekarar 2018Labarai masu alaka