Sharhin Al'amuran yau da kullum

Zanga-zangar rashin aikin yi da talauci a kasar Iran da aka fara a garin Mashhad ya yadu zuwa garuruwa da dama kamar su Nishabur, Shahrud, Kirmanshah, Kum, Rasht, Yazd, Kazvin, Zahidan da Ahvaz .

Sharhin Al'amuran yau da kullum

Da farkon zanga zangar dai gwamanatin kasar ce kawai aka kalubalanta amman daga bisani masu zanga –zangar sun dinga sukar tsarin al’adar kasar. Idan muka dubi garin Kum da ya kasance gari mai tasiri a addinin shi’a, masu zanga-zangar sun dinga rera taken „“bama son Hizbullah“ „“Bama yin Khamenei“ Bayan kame mutane da dama, da yawa mutane kuma sun rasa rayukan su a sanadiyar tarzomar.

 Abin tambaya dai anan ita ce: yaya Iran zata kasance a halin yanzu, shin ko tarzomar zai ci gaba ne ko kuma zai kawo karshe?

Mun kasance tare da Malam Can Acun da ke cibiyar bincike akan Siyasa da Tattalin Arziki watau SETA dake nan Ankara domin kawo muku sharhi akan lamarin.

Idan mu ka dubi Iran da idon basira, za mu ga cewa ta na fama da muhimman matsalolin guda biyu- tabarbarewar tattalin arziki da kuma kalubale a siyasar ta a cikin gida

Da farko dai, adawar siyasa da ke tsakanin Ruhani da mataimakin shugaban addinin kasar Khamenei na kara habbaka tun bayan zaben kasar ta karshe. Zargin da Ruhani ya dinga wa Khanemei da na kusa dashi da laifin cin hanci da rashawa ya sanya zubewar darajar hukumar ga idon da yawan al’umar kasar. Haka kuma, takunkumin da aka sanya wa Iran hadi da rashin iya gudanar da mülki da kuma karuwar rashawa sun sanya tattalin arziki kasar kasance wa cikin ha ula’i. Duk da irin dinbin man fetur da kasar ke mallaka asusun kasar a shekaran bana ya sauka daga dala biliyan 500 zuwa dala biliyan 350. Kasar dai na fama da hau-hawan farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi, gurbatar yanayi da fari. A dayan barayin kuwa dangantakar harkokin wajen kasar naci gaba da gudana ta hanyar yada manufa. Iran dai naci gaba da yada karfin ta da manufofin ta a kasashen waje, kamar su Lebnon, Siriya, Yaman da Iraki sai dai al’umar kasar Iran basu da bukatar wannan tsarin.

Daya daga cikin ababen da suka hura wannan tarzomar dai itace kabilanci, Idan muka dubi yankunan da zanga zangar ta fi kamari kamar Ahwaz zamu ga cewa yankin Larabawa ne, a gabashin Iran kuwa kabilar Baluchis, yammacin Iran Kurdawa da kuma yankin da Turkawa su ke aka fi aiyanar da tarzomar, da hakan ne muke ganin wannan zanga zangar nada alaka da kabilanci.

Ya kamata mu san cewa duk da dai akwai matsalolin cikin gida a sanadiyyar zanga-zangar akwai kuma hannu daga waje. Idan muka duba za mu ga wakilan kasashen waje sun bayyana mutuwar mutane a zanga-zangar a matsayar kissar gilla.. Haka kuma ganin yadda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar ta shafinsa na twitter da kuma farin cikin da shugaban kasar Isra’ila Benjamin Netinyahu ya yi akan yunkurin sun kasance hujjoji da cewa da hannun kasashen waje a tarzomar

Ma’aikatan harkokin wajen Turkiyya ta bayyana cewar akwai bukatar Iran wacce ta ke kawace ta kasance cikin lumana. Sanarwar ta yi kira ga shugaba Ruhani ya dauki matakan tabbbatar da zaman lafiya a kasar sa ba tare da an take hakkin dan adama ba. Haka kuma ta yi kira ga masu zanga-zangar da kada su lalata dokiyoyin kasar da sunan tarzoma. Ma’aikatan ta yi fatar samar da zaman lafiya a kasar tun kafin a samu katsa landan daga waje.

Akwai bukatar mu kalli wannna zanga-zangar da idon basira, musanman kasancewar sa bayan shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da rangadi a kasashen gulf inda ya nemi goyon bayan kasashen Saudiyya, Haddafiyar Daular Larabawa, Misira, Bahrain da Israila domin kalubalantar Irab din.  

A gaskiyar lamari, kasar Iran ta kasance cikin matsaloli da wasu kasashen waje, hakan kuwa na da nasaba da halin da kasar ta ke ciki yanzu. Mataimakin shugaban kasar na farko Ishaq Chihangiri a ya bayyana cewar bawai matsalar tattalin arziki kawai ke haifar da zanga zangar ba, da ma wasu dalilan a bayan fage. Kamar yadda wata jarida mai goyon bayan gwamnati ta wallafa a shafin ta ta farko- wasu da ke neman cimma burin su ke jagorantar zanga-zangar.

Haka kuma Ayetullah Hammaney ya bayyana cewar wasu makiyan mu na raba kudi, da makamai domin haifar da tarzoma a kasar mu.

Amman kuma makiyar Iran, na kallon lamarin akan yaduwar talauci a kasar duk da din bin arzikin da ta ke dashi.

‘Yan zanga-zangar sun dinga fadar “ku daina kashe kudin mu a Siriya” ku rabu da Siriya mu ku kula damu, “Ba Gazza, Ba Siriya, Ba Hizbullah” sun kasance muhimman taken da masu zanga zangar su ka dinga rerawa. Hakan dai na nuni da yayinda Iran ke fama da matsalolin tattalin arziki a cikin gida ta maida hankalin ta wajen yada akidojin ta a gabas ta tsakiyya, an bayyana cewar wadanda ke gudanar da yaki da izinin Iran a Siriya na karbar albashi fiye da mafi yawancin ma’aikatan kasar.

Bugu da kari, masu gudanar da zanga-zangar sun kara da cewa “Bama son daular Musulunci” Ba mamaki dai ga yadda su ka dinga addu’a ga wanda ya jagoranci kasar bisa ga akidar kasashen yamma Riza Shah Pehlevi.

Hakikanin gaskiya dai, zanga-zangar kasar Iran a bangare guda yana da nasaba da halin tattalin arzikin da kasar ke ciki, a dayan barayin kuma da hannun wadanda suka kasance makiyar kasar a fadin duniya.Labarai masu alaka