Manufar Turkiyya a kasashen ketare

Jama'a barkanmu dai, da kuma sake kasance wa a cikin sabon shirin batutuwan manufar Turkiyya a kasashen waje.

Manufar Turkiyya a kasashen ketare

A ‘yan kwanakin da suka gabata shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğanya kai ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka 3. A wannan mako za mu yi nazari kan yaddda wannan ziyara ta shafi manufofin Turkiyya a kasashen waje. Za kuma mu yi sharhi kan jawabin malami a sashen nazarin alakar kasa da kada da ke jami’ar Ataturk ta birnin Erzurum na Turkiyya.

A tsakanin ranakun 24 da 27 ga watan Disamba shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ziyarci kasashen Sudan, Chadi da Tunusiya. Manufar ziyarar shi ne a kara zurfafa manufofin Turkiyya a Afirka tare da haba alakar tattalin arziki da sauransu tsakanin kasashen 3da Turkiyya. Kasa ta farko da Erdoğan ya fara zuwa a Afirka  a wanna lokacin ita ce Sudan. Sudan kasa ce daga cikin manyan kasashen nahiyar Afirka. Kasa ce da ta kasance karkashin matsi da takunkumin tattalin arziki a cikin shekaru 20 da suka gabata. Bayan an janye takunkumin an samu kamfanunnuka da dama da suka koma Sudan.

Yadda Erdoğan ya ziyarci Sudan da ‘yan kasuwa kusan 200 abu ne da ya sanya farin ciki. Ministocin kasashen 2 sun sanya hannu kan yarjeniyoyi 13 da suka shafi cigaban tattalin arziki, raya al’adu da siyasa. Al’umar Sudan sun nuna wa Erdoğan kauna ta hanyar ta hanyar fita kan tituna da tutocin kasar Turkiyya.

A yayin ziyarar ta Sudan shugaba Erdoğan ya ziyarci tsbirin Sevakin wanda wani bangare ne na Daular Usmaniyya a wancan lokacin. Ya duba aikin farfado da tsibirin da Hukumar Cigaba da Hadin Kai ta Turkiyya TIKA ke yi. Erdoğan ya bukaci shugaban kasar Sudan Umar Al-Bashir ya ba su dama su gyara tsibirin sosai. Al-Bashir ya amince da bukatar Erdoğan tare da ba wa Turkiyya wannan dama.

Sevakin tsibiri ne mai tashar jiragen ruwa wanda ke da matukar muhimmanci ga jama’ar Masar da Siriya a gabar Red Sea da ya kasance karkashin Daular Turkawa. A karni na 15 da ‘yan mulkin mallak ana portugal suka kai hari a yankunan Red Sea da ke Yammaci da Gabashin Afirka sun lalata wurare da dama inda suka kuma kafa shugabanci bayan kawar da sarakunan yankin. A shekarar 1513 ne Sevakin ya koma karkashin mutanen Portugal. A lokacin mülkin Sarki Sultan Yavuz Selim ya yaki ‘yan portugal a wannan yanki bayan ya kwase Masar da Siriya tare da kafa mülki a gabar tekun Red Sea. Ya kubutar da yankin daga mamayar ‘yan mülkin mallak ana Portugal.  

Turkiyya ta hanyar amfani da TIKA za ta dawo da Sevakin mai tarihi zuwa cikin hayyacinsa. Yankin zai samu habakar kasuwanci da yawon bude ido. Turkiyya da Sudan za su hada kai wajen samar da tsaro a yankin na tekun Red Sea. Ta hakan za a iya cewa, nan da wani dan lokaci Turkiyya za ta samar da zaman lafiya a Yaman da Somaliya.

Bayan kasar Sudan shugaba Erdoğan ya wuce zuwa Ndjamena babban birnin kasar Chadi. Lakar Turkiyya da Chadi ta samo asali tun karni na 16. A ‘yan shekarun nan alakar kasashen 2 ta bunkasa sosai. Tsohon Firaministan Chadi  Kalzeubé Payimi Deubet ya ziyarci Turkiyya a tsakanin ranakun 15 da 18 ga watan Disamabn 2014. A lokacin wanna ziyarar an sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama. A yayin ziyarar ta Chadi da Erdoğan ya kai akwai shugaban rundunar sojin Turkiyya Hulusi Akar. Wannan ziyara na da matukar muhimmanci ganin yadda Chadi a ‘yan shekarun nan ta ke yaki da ta’addanci a yankin. Yarjeniyoyin da aka sanya hannu a kai tare da taron hadin gwiwa na kasuwanci za su habaka alakar turkiyya da Chadi.

Alakar Turkiyya da Tunisiya da ta samo asali tun tale-tale na ci gaba da bunkasa. Manyan Wakilan kasashen biyu na yawan ziyartar juna a kai a kai. Suna tuntuba da shawartar juna a kowanne bangare. Yadda daular Turkiyya ta yi shekaru 300 tana shugabantar Tunisiya ya sanya jama’ar kasar jin suna da kusanci da Turkiyya sosai.

A tsakanin 24 da 25 ga watan Disamban shekarar 2012 Shugaban gwamnatin Tunisiya na lokacin Hammadi jebali ya ziyarci Turkiyya.  A lokacin majalisar hadin kan kasashen ta amince kan yarjejeniyar siyasa. A ranakun 5 da 6 ga watan Yunin 2013 shugaba Erdoğan ya ziyarci Tunisiya inda wannan majalisa ta yi taronta na farko. A lokacin an sanya hannu kan yarjeniyoyi 21 da tsare-tsare 24 don cigaban garuruwan kasashen 2. Ziyarar ta karshen 2017 ta sake zaunar da yarjejeniyar sosai.

Kafin wannan, a shekaru 10 da suka gabata a kwai zargi da kokwanto game da alakar turkiyya da kasashen Afirka. Amma a yanzu duk babu wannan abu. Yanzu dai Turkiyya na nuna damuwa a Afirka sosai. Turkiyya na bayar da muhimmanci sosai ga siyasa, al’adu, aiyukan soji da tattal,n arzikin Afirka. Yadda a Afirka ake nuna kauna ga Turkiyya ba a nuna wa wata kasa a yammacin duniya ko kasa ta Musulunci. Yadda shugaba Erdoğan ya kai batun “Afirka ta warware matsalolinta da kanta” yana samun karbuwa a nahiyar.

A yanzu shugaba Erdoğan ya kai ziyara zuwa kasashen Afirka 28. A yanzu kamfanin jiragen sama na Turkish Airlines na zuwa garuruwa 51 a kasashen Afirka 31. Asusun Ma’arin na aiyuka a kasashen Afirka sama da 6.  Yadda hukumar TIKA da Kungiyoyin farar hula na Turkiyya suke aiyuka a nahiyar na taka rawar gani sosai wajen karfafa wannan alaka. A yanzu alakar kasashen duniya na da muhimmanci sosai a fasgen nazarin alakar kasa da kasa. Turkiyya na gabatarwa da Afirka manyan damarmak, na cigaban siyasa, tattalin arziki da raya al’adu. Kamar yadda muke ganin shugaba Erdoğan na ta yin aiyuka don tabbatar da haka inda y ke zuwa kasashen Afirka ya dawo gida Turkiyya lafiya.

 Labarai masu alaka