Mahangar Gabas ta Tsakiya daga Turkiyya

Kusan kowa yasan cewa babu riba ga yunkurin shugaba Trump na mayar da Qudus babban birnin Isra’ila, ta bada umurnin canja ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin da sunan taimakawa Isra’ilawa da su ka kwashe shekaru su na zalunta da kalubalantar Falasdinawa

Mahangar Gabas ta Tsakiya daga Turkiyya

Sakamakon wannan yunkurin yayi dai-dai da zaben raba gardamar da Barzani ya gudanar a Arewacin Iraqi. Haka kuma, wannan wutar kin kari da Trump ya hasa a Gabas ta Tsakiya ko shakka babu kyaikayi za ta koma kan mashekiya.

Da jagorancin Turkiyya ne kungiyar tarrayar kasashen Musulmi ta gudanar da taron gaggawa a ranar 16 ga watan Disambar shekarar 2017 a Istanbul. Wannan taron dai ita ce ta farko da kasashen musulmin suka gudanar da gagarumin taron da ke nuna irin hadin kan da ke tsakaninsu. Wannan ne dai mataki na farko acikin karni biyu da kasashen Musulmi su kayi gangami domin kalubalantar kalubalen Amurka da Isra’ila. Abu mafi muhinmanci awannan taron dai shi ne- nuna cewa musulmi na iya hada kan su duk da matsalolin da ke tsakanin su, yunkurin kasashen Musulmi karkashin jagorancin Turkiyya ya karya kashin bayan manufar Amurka da Isra’ila akan Qudus. 

Duk da irin rigingimun da ke addabar kasashen Musulmi, kamar su Siriya, Yaman da Libiya, rikicin addini da mazhabobi da ke tarwatsa duniyar Musulmi, ‘yan ta’addar DEASH da su ka zama alakakai, rigingimun kasashen gulf, juyin juhanin kasashen larabawa, kalubalen da mulkin Sisi ke fuskanta a Misira, yunkurin murabus din Firaministan Lebanon a Saudiya dama sauye-sauyen da Saudiya ke famar yi acikin gidan ta; Kasashen Musulmin sun gudanar da taron da su ka dauki mataki mai tasiri, hakan na nuni da cewar akwai haske ga yadda kasashen musulmin za su kasance anan gaba.

Duk da haka, babu wani shugaba ko wakilin shugaba daga kasashen Larabawa da ya yiwa al’umar kasarsa jawabi akan yadda Qudus za ta kasance idan aka mika ta ga Isra’ila- wannan dai irin yunkurin Malik Kamil ne a karni ta tsakiya. Tarihi ya nuna cewa domin kwadan mulki Malik Kamil ya mika Qudus ga Yahudawa; birnin da Sultan Selahaddin Eyyup ya karbo bayan shekaru 88 a shekarar 1187. Hakika Malik Kamil ya la’antu daga Musulman wannan karnin tun daga Bagdad, Cairo zuwa Damascus. A bisa wannan dalilin ne babu wa ta kasar Larabawa da ta jefa kuri’ar goyun bayan Isra’ila domin hakan zai haifar da wa ta juyin juhanin kasashen Larabawa kashi na biyu da ka iya kawo karshen gwamnatocin da ke tangadi. 

A dalilin jagorancin da Turkiyya ta yiwa kasashen Musulmi, duk da kalubalen Amurka da Isra’ila kasashen sunyi shuri da yunkurin ta shugaba Trump. Idan muka duba za muga cewa kananan kasashe wadanda ma ba’a san su sosai ba suka goyi bayan yunkurin, a yayinda wadanda su ka kaurace ma zaben mafi yawan su kasashen yankin Hawaii ne kamar su Antigua, Bahamas, Benin, Bhutan, Equatorial Guinea, Rwanda, Solomon Islands, Tuvalu da Vanautu. Hakan na karantar da kudi ba zai biya ko wacce bukata ba, ganin Trump ya yi ikirarin yanke tallafin da Amurkan ke baiwa wa su kasashe idan ba su bi ra’ayin sa ba akan Qudus.   

Idan muka yi la’akari da sakunan da Trump ke yadawa a shafukan twitter sa ga dukkan alamu bai san takon sakan gabas ta tsakiya da kasashen Musulmi ba, a dalilin hakan ne matakin na sa ya kasa haifar da da mai ido, sai ma shafawa kansa kashin kaji ya yi. Taron kolin kasashen Musulmi da Turkiyya ta jagoranta a Istanbul da zaben da MDD ta gudanar ya wotar da hakincin da Amurka ke kokarin yi a fadin duniya. Hakan dai na ishara ga samun kubutar gabas ta tsakiya da kuma nuni da yadda tsarin duniya ta ke yanzu ka iya canzawa. Hakan kuma na nuni ga samun ‘yanci mai inganci ga wasu kasashe. Zamu dai sa ido mu ga yadda lamurka zasu kasance a kwanakin da ke tafe.              Labarai masu alaka