Tarihin Sarki Midas da ya yi mulki a Turkiyya

A cikin shirinmu na wannan mako, zamu baku labarin tarihi sarki Midas na mutanen Frig mai kayatarwa shi ya sa ku nemi kujera ku zuwa domin jin tarihin al’amurran da suka faru a wannan lokaci.

Tarihin Sarki Midas da ya yi mulki a Turkiyya

A cikin shirinmu na wannan mako, zamu baku labarin tarihi sarki Midas na mutanen Frig mai kayatarwa shi ya sa ku nemi kujera ku zuwa domin jin tarihin al’amurran da suka faru a awnna lokaci.

A cikin karni na 11 kafin miladiyya, mutanen Frig sun fita daga Trakya suka zo kusa da Ankara inda suka kafa cibiyar Gordion na gwamnatinsu. Masana’antu da aka kafa ne ya sa a cikin ‘yan karamin lokaci sai kasar ta samu cigabada ariziki mai yawa. Sune al’umar da suka fara samar da tagulla wanda a ko’inan duniya ake anfani da shi kuma sun samu ci gaba a wurin wannan aiki. A yau sune jijiyar fasahar da ake fara anfani da shi tun shekaru dubu 3’un da suka gabata. Su ne mutanen da suka samar da allura, cokali da kuma wasu abubuwa daban-daban. Sarkin Midas ya kasance wani dan kauye ne wanda shi da iyalensa suke zama a kauyen inda ya zama babban mutum bayan ya shugabanci mutanen Frig inda suka yi nasarar yakin gabar tekun Mediterrenean. Hakan ya faru ne a lokacin da suka dauki hanya zuwa arewa sai sarkin mutanen Frig na wannan lokaci Gordios ya rasa ransa. Da yake mutanen na matukan son sarkin, shi ya sa sai mutuwarsa ya zamo musu bakin ciki sosai. Shi ya sa sai manyan mutane suka gana da boka domin su zabar da sabon sarki. Sai bokar suka fada musu cewa, farkon mutumin zai shigo garin da irin motar wannan lokaci shi ne zai zama sarki. Nan ba da wani lokaci ba sai Midas tare da iyalensa suka dawo daga tafiyar da suka yi inda suka shigo cikin garin. A dai-dai wannan lokaci ne al’ummar kasar suka yi matukan farin ciki da zuwarsa domin shi ne alamar sarkinda suke jira. Wannan al’amari ya ba Midas da iyalensa matukar mamaki domin ba su san dalilin da ya sa ake tarbesu haka ba.

Sabon sarki Midas yayi nasarar mulkin kasar karmar yadda aka bukatar yayi. Amma sai dai sarki Midas tun da aka haifeshi sai kunensa daya ya fi daya girma. A tunanensa wannan dayan kunensa da yake da girma wani alama ce da ke nuna muninsa shi ya sa a kowannen lokaci yana sanya hula saboda ya rufe kunnuwarsa. A cikin wasu ‘yan lokuta sai mutanen kasar suka fara yarda cewa sarki Midas na da kunnuawar jaki ne domin basu taba ganinsa ba hula a kansa ba. Tarihi ya kuma nuna cewa sarki Apollon wani mutumi ne da yake kada garaya a lokacin da suke hutu. Da yaga mutane sun fara sukarsa cewa yana kwaikwayon mugu hali a kowanne lokaci inda yana kada garaya shi ya sa sai fusata ya jefa garayar cikin kogi. Bayan ya jefa cikin kogi sai wani mai kiwon dabbobi Marsias ya sinti inda shi ma ya fara kadawa. A cikin ‘yan karamin lokaci sai kowa ya fara maganarsa akan yadda ya iya kada garayar. Sai kowa ya fara maganar yadda yake kada garayar. Da Apollo ya samu wannan labari sai ya je ya samu Midas ya yanke hukuncin al’amurra da suke faruwa inda Midas ya je zai gudanar gasa tsakanin Apollo da makiyayin dabbobin. A yayin gasar sai sarki Midas ya zabi makiyaye matsayin gwanin gasar. Sai Apollon ya bukaci a gudanar da gasar ta wani hanya daban inda sai yayi nasarar gasar. Apollon ya fusata a lokacin da Midas ba zabi wakarsa a matsayin wakar da ya fi kyau ba inda ya zagi Midas da cewa, “ kunenka bai da kyau shi ya sa ka kasa gane kidi mai kyau daga mara kyau, kamata ne a baga kunen jaki” ta haka ne sai mutanen suka fara tunanen cewa ya kwatanta kunen Midas da kunnen jaki. Apollo na fadin haka sai kunya ya kama Midas inda ya kasa fitar da hularsa. Sai wata rana ya kira wanzami domin ya haske masa gashinsa. Wanzamin na ganin gashinsa sai ya tsorata kuma abin ya bashi mamaki. Sai Midas kuma ya gargadeshi cewa idan ya kuskura ya fadima wani abinda ya gani to ya ci alwashin sai ya kasheshi. Ana-nan anan-nan sai wannan al’amari ya sa wanzamin rashin natsuwa domin yana son ya fadima wani abinda ya gani a gefe guda kuma sai ya tsoron mutuwa. Sai wata rana kawai sai ya je ya saka kanshi cikin rijiya inda ya je “kunen Midas yayi kama da na jaki.” İrin yadda ya yi ihu a yayi maganar sai ya zama kamar abinda ya fadi maimatashi ne. Ta haka ne mutane suka fara fadiwa juna abinda suka ji inda a cikin ‘yan karamin lokaci sai mutane da dama suka gano cewa kunnen Midas yayi kama da na jaki.

Wani tarihi mai kayatarwa na biy u game da Midas da muks son mu baku labarin shi ne, Midas wani mutumi idan ya taba komai sai ya juya zinariya. Wata rana a cikin yawon da mashayi Dionysos yake yi sai barci ya daukeshi a wajen gidan Midas. A lokacin da ya tashi daga barci sai sarki ya karbi bakuncin shi da abokansa. Irin karamcin da Midas nunawa Dionysos ne ya sa sai ya ce masa, “roki dukkan abinda kake so daga wuri na, ni kuma zan biya maka bukatarka. Da yake Midas na son zinariya sosai sai ya bukaci dukkan abinda ya taba ya juye zinariya. Inda Dionysos kuma ya cika masa burinsa. Ana-nan ana-nan sai dukkan abinda ya Midas ya taba da hannunsa sai abin ya juye zuwa zinariya. A cikin ‘yan karamin lokaci sai wannan al’amari ya zama tashin hankali ga Midas domin baya iya komai. Ko abinci ma baya iya ci domin da zaran dauki cokali sia ci abinda zi cokalin ta juye zinariya. A wurin ya gano cewa yayi kuskure wurin roko, sai ya je ya sami Dionysos domin ya ceceshi game da al’amarin da ke faruwa ga shi. Sai Dionysos kuma ya ce masa idan yana son ya kubuta daga wannan al’amari sai ya je yayi wanka a kogin Gediz da ke Paktalos. A lokacin da yaje yayi wanka a wurin, sai ya kubuta daga wannan al’amarin da ya faru gareshi. A yayin da yake wakar a cikin kogin zinariyar da ya fita daga jikinsa ya zama sanadiyyar da aka samu zinariya a cikin kogin na wani tsawon lokaci.


Tag: Midas , Gediz

Labarai masu alaka