"Ku bar murna,karenku ya kama zaki"

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka,Heather Nauert ta ce,kamata yayi duniya ta daina zargin Bin Salman da kisan Kashoggi,saboda akwai tambayoyi da dama wadanda kawo yanzu ba a samu amsoshinsu ba.

"Ku bar murna,karenku ya kama zaki"

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka,Heather Nauert ta ce,kamata yayi duniya ta daina zargin Bin Salman da kisan Kashoggi,saboda akwai tambayoyi da dama wadanda kawo yanzu ba a samu amsoshinsu ba.

Nauert ta ce, rade-radin da a yanzu haka ake ci gaba da yadawa na cewa Fadar House ta gano kwararan hujjojin da ke nuna cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya ne ke alhakin kashe dan jarida Jamal Kashoggi,kanzon kurege ne.

Kakakin ta wallafa wata rubutacciyar sanarwa bayan ganawar da ta yi da ministan harkokin wajen Amurka,Mike Pompeo,shugaban Hukumar Leken Asiri ta CIA,Gina Haspel kan batun kisan Basa'udiyyen dan jaridan,inda ta ce

"Amurka ta yanke shawarar hukunta duk wanda ke da hannu a kisan Kashoggi.Amma dukannin labaran da yanzu ake ci gaba da yadawa game da kwakkwarar hujjar da fadar White House ta cimmawa kan wannan batun zuki-ta-malle ne.Saboda akwai tambayoyi bila-adadin wadanda kawo yanzu ba a samu amsoshinsu ba.Sanin kowa ne,mun kakaba wa mutane 17 wadanda ke da hannu a mutuwar Kashoggi,takunkumi.Matakinmu na gaba shi ne, gano wadanda suka kitsa da kuma kashe dan jaridan.Zamu ci gaba da yin taka-tsantsan yayin gudanar da wannan aikin,don kare alakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya".

A jiya ne dai CIA ta sanar da cewa,Muhammad Bin Salman ne ya bada umarnin kashe Kashoggi.Amma ga dukannin alamu gwamnatin Washington ba ta da aniyar jauya wa babbar kawarta a yankin Gabas Tsakiya,baya.Labarai masu alaka