Fasfon da ya fi kima da karfi a duk fadin duniya

Hukumar tantance kima da karfin fasfuna kasashen duniya, Henley Passport Index ta ayyana fasfon da ya fi kowanne kima da karfi a duk fadin duniya na shekarar 2018.

Sakamakon da Henley Passport Index ta wallafa, a jerin fasfuna 199 da aka auna martabarsu,ta kasar Japan ta ci tuta,inda ake iya shiga da fasfonta a kasashen 189 ba tare da biza ba.

Kasashen Jamus da Singapur sun mara ma ta baya a matsayi na 2,inda ake iya amfani da fasfunansu don shiga kasashen duniya 188 ba tare da biza ba.

A matsayi na 3 akwai Koriya ta Kudu,Finland,Faransa, Italiya,Spain da Sweden.Labarai masu alaka