Jagoran Falasdinawa ya mutu a gidan kurkukun Isra'ila

Wani jagoran Falasdinawa mai shekaru 53 da ke daure a gidan kurkukun Isra'ila Aziz Aviysat ya mutu.

Jagoran Falasdinawa ya mutu a gidan kurkukun Isra'ila

Wani jagoran Falasdinawa mai shekaru 53 da ke daure a gidan kurkukun Isra'ila Aziz Aviysat ya mutu.

Sanarwar da Kungiyar Jama'ar Falasdinawa da aka Kama ta fitar ta ce, Aviysat na kwance a asibitin gidan kurkukun Al-Ramla bayan zuciyarsa ta samu matsalar gudanar jini kuma bayan an yi masa dashen zuciya a asibitin Assaf Harofeh ya mutu.

Kungiyar ta ce, gwamnatin Isra'ila ce ke da alhakin mutuwar Aviysat inda suka zargi masu kula da gidajen yarin wajen gaza ba shi magunguna.

Tun shekarar 2014 aka kama Ayivsat tare da daure shi na shekaru 30 a gidan kurkukun Isra'ila.

Kungiyar Hamas ta dora alhakin mutuwar dattijon kan Isra'ila.

Kakakin Hamas Hazim kasim ya fitar da sanarwa cewa, wannan zalunci da ake yi wa mutanensu da aka kama ba zai karya musu gwiwa ba. Wannan wata ta'asa da ake yi wa Falasdinawa.

Sojojin Isra'ila sun tarwatsa Falasdinawa da suka yi zanga-zangar la'antar mutuwar jagoran nasu a kurkun Yahudawa.Labarai masu alaka