Erdoğan: Amurkace ke goyon bayan kungiyar ta'addar FETO

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar Amurkace ke goyon bayan kungiyar ta'addar FETO.

Erdoğan: Amurkace ke goyon bayan kungiyar ta'addar FETO

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar Amurkace ke goyon bayan kungiyar ta'addar FETO.

A yayinda ya yi tambaya ga Amurkan da cewar "Me yasa ba zaku kori shugaban 'yan ta'addar FETO daga kasarku ba?"

Erdoğan dake amsa tambayoyi a gidan wani talebijin mai zaman kansa, yayi korafi akan yadda shugaban kungiyar ta'addar FETO ke zaune a katabaren wuri a Amurka, inda yake cewa "Amurka sun maidashi tamkar dansu, inda suka ki fitardashi daga kasarsu duk da dalilan da aka bada akan laifukan daya aikata, hakan na nuni da Amurka bata mutunta yarjejeniyar dake tsakaninmu"  

A yayinda shugaba Erdoğan ke bayyana cewar an mikowa Turkiyya mambobin 'yan ta'addar FETO guda 83 daga kasashen waje, ya tabbatar da cewa za'a ci gaba da bin sawun 'yan ta'addar aduk inda suke.

Shugaba Erdoğan ya bayyana iya adadin 'yan ta'addar da aka kashe tun bayan soma fattatakar 'yan ta'addar PKK/PYD-YPG. Inda ya bayyana cewar an kashe 'yan ta'adda dubu 4 da dari 254 a Afrin dake Siriya, haka kuma hare-haren da aka fara a ranar 10 ga watan Maris a arewacin Iraqi anyi nasarar kashe 'yan ta'adda 346, a cikin gida kuwa an kashe 240.

Shugaba Erdoğan ya jaddada aniyar kasar akan ci gaba da yaki da ta'addanci cikin gida da kuma waje.Labarai masu alaka