Abbas: "Zamu ci gaba da kalubalantar Trump akan Qudus"

Shugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas ya bayyana cewar ba zasu taba yarda wata kasa ta mayarda ofishin jakadancinta a Qudus a matsayar birnin Isra'ila ba.

Kamar yadda kanfanin dillancin labaren Falasdinu WAFA ya rawaito, shugaba Abbas ya fito karar ya bayyana cewar "Ba zamu saka ido mu kyale Donald Trump ya mayarda ofishin jakadancin kasarsa a Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila ba".

Inda ya kara da cewa "Falasdinu zata ci gaba da kalubalantar lamarin, har sai an kawo karshen rikicin Falasdinu-Isra'ila.

A yayinda yake kira ga samar da kasa biyu domin warware rikicin, ya kara da cewa: "Qudus cibiyar addinin Ibrahimiya ce da suka hada da Islama, Kiristanci da Juda. Mabiya wannan addinin ka iya zuwa suyi ibadarsu ba tare da tsangwama ba. Munyi ta nanata cewar gabashin Qudus itace babban birninmu kuma a bude take ga kowa"

Daga karshe Abbas yayi kira ga dukkanin musulmi da su ziyarci Qudus.

A ranar 6 ga watan Disambar 2017, Trump ya bayyana Qudus a matsayar babban birnin Isra'ila lamarin da ya janyo kace-nace tsakanin kasashe tare da haifar da gudanar da zanga-zanga a Falasdinu.

 Labarai masu alaka