Putin da Ruhani sun tattauna game da Siriya

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Iran Hassan Ruhani inda suka duba batun hari da makamai masu linzami da Amurka ta jagoranta wajen kai wa Siriya.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar Rasha ta fitar ta ce, shugabannin 2 sun amince kan cewa, hare-haren ta sama sun lalata kokarin samar da zaman lafiya a Siriya.

Putin ya ce, idan har aka ci gaba da yin irin haka ana karya dokar majalisar Dinkin Duniya to za a samu matsalar dangantakar kasashe a matakin kasa da kasa.

A ranar Asabar ne Amurka, Ingila da Faransa suka kai wa Siriya hari da makamai masu linzami sakamakon hari da makami mai guda da ta kai a yankin DUma na Gabashin Guta.

Putin da Ruhani sun kuma tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya musamman ma Kasar Yaman.Labarai masu alaka