Sarki Salman ya yi wa Trump ahir

Mai martaba sarki Salman bin Abdul-Aziz na Saudiyya ya tallafa wa Falasdinawa da dalar Amurka milyan 150 ,kana ya ce sai dai a kashe tsohuwa kan daddawarta, domin ba zasu taba yarda Trump ya maida tsarkakken birnin Qudus, helkwatar kasar Yahudu ba.

Kral Selman.jpg
suudi arabistan kralı.jpg

Mai martaba sarki Salman bin Abdul-Aziz na Saudiyya ya tallafa wa Falasdinawa da dalar Amurka milyan 150 ,kana ya ce sai dai a kashe tsohuwa kan daddawarta, domin ba zasu taba yarda Trump ya maida tsarkakken birnin Qudus, helkwatar kasar Yahudu ba.

Sarki Salman ya furta wannan kalamin a ranar Lahadi din nan da ta gabata, a wani jawabin share fade da ya yi a taron kungiyar kasashen Labarawa da aka gudanar a birnin Dhahran na gabashin Saudiyya.

Mai martaba ya mika wa kungiyar Jerusalem Islamic Waqf wacce ke kula da tsarkakkun wuraren Islama da Gabashin Qudus,zunzurutun kudi dalar Amurka milyan 150.

Haka zalika ya bai wa ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira a Falasdinu (UNRWA), dalar Amurka milyan 50.

A yayin da yake magana Sarki Salman ya ce,

"Ahir ga Amurka.Sai dai aka kashe tsohuwa kan daddawarta.Ba zamu taba yarda Qudus ta koma helkwatar Isra'ila ba.Falasdinu da al'umarta na cikin zuciyar illahirin Larabawa da Musulmai", kuma wata rana za su shirya wani taro mai taken "Taron Qudus".

Shugabannin kasashe 16 na Larabawa ne suka halarci wani babban taro wanda aka shirya  a washegarin farkaman bai daya da Amurka, Faransa da Ingila suka kai wa gwamnatin Sham,wacce ake zargi da yin amfani da makami mai guba.

A taron an tattauna matsalolin kasashen Siriya da Falasdinu da kuma sukar Iran,wacce ke ci gaba da shisshigi da  dagula lamurra a yankin Gabas ta Tsakiya.

Taron na Lahadi an shirya sa ne watanni uku kacal bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ayyana Qudus a matsayin helkwatar Isra'ila.Wanda hakan yasa duniya ta yi caa kansa.

AALabarai masu alaka