Ruhani: Ya kamata Sunni da Shi'a sun zama tsintsiya madaurinki daya

A yayin wata ziyara da kai kasar Indiya shugaban Iran, Hasan Ruhani ya gayyaci Musulman duniya da su yi watsi da gaba da mazahabanci don rungumar juna.

da yake jawabi a gaban Muslman yankin Hedarabad,shugaban na Iran ya ce :

"Kamata yayi Muslman duniya su yi watsi da duk wata gaba,kabilanci da kuma mazahabanci don rungumar juna.Saboda rashin hadin kai ne ya jefa Falasdinu halin ha'ula'i.Makiya Islama na ci gaba da gwagwarnmaya dare da rana, awajen ganin sun yada fitina da tashin hankali tsakanin Musulmai tare da shafa wa tarihinsu bakin fenti.A wannan garin na Herabad akwai Sunni da kuma Shi'a.Wannan ba wata matsala ba ce, kamata yayi mu hada karfi da karfe don cigaba da daukakar Islama"

Tag: Indiya

Labarai masu alaka