• Bidiyo

"Dole ne Amurka ta shirya gwabzawa da China"

Shugaban Rundunar sojojin Amurka,Harry Harris ya ja hankalin 'yan majalisar dattijan kasarsa game karfin sojan China,inda ya ce lokaci ya zo da kamata a ce mun shirya fafata yaki da Sin.

A cewar Harris wanda aka nada a matsayin jakadan Amurka a Australia,dole ne su daura damarar fafata yaki da China.Saboda a yanzu haka, Sin na ci gaba da ninka karfin sojinta.Haka zalika saura kiris, rundunar sojojin China ta zarce tasu a kowane fanni.

Shugaban rundunar ya jaddada cewa, yana matukar tsoron ganin China ta dagule ka'idojin kasa da kasa da aka shimfida tun shekaru bila adadin a fannin soja.

A ranar 2 ga watan Fabrairun bana, ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta wallafa wani jerin sunayen kasashen da ta ayyana a matsayin barazana ga tsaron kasarta,wanda ke kunshe da sunayen  Rasha,China da kuma Koriya ta Arewa.                                                                                                                                                                                                                                                                   

Tag: Amurka

Labarai masu alaka